Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBEYou Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namuAlura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOCMasu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our servicesNote that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame usNote that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download itNote that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTThis Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🏡A WANI GIDA🏡


LABARI /RUBUTAWA
KHADIJA S. SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)


GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, wanda shiya aiko Annabi MUHAMMAD (SAW) da shiriya. Allah ya shiryemu baki daya ameen.


SADAUKARWA
Na sadaukar da dukkan wannan littafi ga al’ummar misulmai baki d’aya.

JINJINA👍👍👍
Jinjina gareku mahaifana, Inamai addu, ar Allah yarabamu lafiya ya saka muku da alkairi ameen.

TA DABAN CE😘😘
Aunty Ameena Khabir kina qaran qwarin gwiwa, Allah yaraya iyalanki.


GABATARWA
Wannan labari qirqirarren labari ne, banyishi dan ko wata ba, na yishi da fadakar, ilimantar, nishadantar, tsoratar da al’umma inason idanan kaga abinda yadace kayi qoqarin aikatawa domin gobenka, abinda nai ba dai dai ba kayi qoqarin gyaramin saboda na qaru wasu ma su qaru, Nagode🤝.


🏡A WANI GIDA🏡

🅿️1️⃣

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN QAI.”Kai!.....Nidai naga ta kaina,kullum neman hanyar da zan samu farin cikin rayuwa nake amma inaa kullum baqin ciki ke kusantata nikam yazanyi ne naji dad’i?”

Hajiya NAFI ce taketa zance ita kad’ai kai idan baka luraba saikace ita da wani takeyi ba ita d’aya ba,miqewa tayi tafara zagaye d’akin tana bin ko’ina da kallo tare da yamutsa fuska tana jan dogon tsaki.

”Hajiya ! Hajiya!! ”kira ya doki cikin kunnuwanta aikam arazane ta juyo tana kallon me kirannata.

”Tsssummmmm, Har me zaki bani kike qwalamin wannan kiran? Ko kinmanta da yanayin danake ciki ne kikazo ki kuma d’agamin hankali?”

”A’a hajiya ba haka...”

”Rufamin baki bahaka bane me? idan ba haka bane tomenene? HAFSA tinbayauba na lura da take-takenki gaba d’aya kuma wallahi munkusa musa qafar wando d’aya dani dake tsuummmm”
Hajiya tayi tsaki sannan tafice tabar falon gaba d’aya.

”Ikon Allah! Lallai naga alamar nima saina tashi tsaye agidannan idan bahakaba to naga alamar Hajiya saita takani nikuma abinda bazan d’auka ba kenan”
Hafsa ta fad’a tare da miqewa itama tafice afalon.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Dad’ina dake LUBA bakya ganewa kullum idan anmiki karatu bakya d’auka kinta inda-inda kamar wadda taiwa sarki qarya”

”Haba HABI kema kinsan kaina yana ja sosai kawai dai kedince kullum abinda zaki zowa da mutum daban kinga dole kansa ya kulle ”

Luba ta bawa Habi amsa.

”Salamu alaikum!”
”Waalaikissalam”
Suka hada baki wajan amsa sallamar,Luba ce tamiqe da sauri tana fad’in,
”Lale Lale yarona sannu da zuwa yimaza kaje kace LARAI ta baka abincinka kaji”

”Tom mama ”
Yaron yafada yana fita sam baima kula da Habi da take zaune ba yau ficewarsa.
”Lallai Luba yaronnan yayi saurin girma tabd’i,uhummm koba Haneef baneba?”

”Uhummn kedai bari Habi wallahi ni kaina abin yanzu yafara bani tsoro,tin ana fad’a ina qaryatawa yanzu harna fara yarda,yaro shekara tara amma kamar me shekara sha biyar ko sama?”
”Ato agaskiya Luba kinemawa d’anki magani dan gaskiya ni ganinsama tsoro yake bani gaba d’aya gashi idan ya kalleni hantar cikinama kad’awa takeyi saboda tsoro”

”Habi Daman kinzo gidannan ne saboda ki qaran d’agan hankali?Dake zanji koda waccan Matsafiyar zanji?Niyau banyi farin cikin zuwankiba akan Haneef zan iya bada raina dan haka kificemin agida tinkafin raina ya b’aci”

Ta fad’a tare da nuna mata hanya alamar ta fice.....

Aikam ba musu sumsum tafice daga d’akin tana kallonta sama da qasa.

🤦🏻‍♀️Wayyo ni Luba meke shirin faruwa dani ne?
Nima lamarin yaronnan yana ban tsoro,kai gashi naga kullum abin gaba yakeyi dole na koma gurin QAURA naji kodai musanyamin yaro na yayine?
Tafad’a tana dafa kai tare da cizon le’be.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”KULU Wallahi tsoron shiga nakeji bakiji yadda gabana yake fad’uwaba”
”Haba HAFSA mene abin tsoro aciki nifa banajin tsoro kijima na fad’amiki ninan da kika ganni KAINUWA CE DASHEN RABBU dan haka ba wanda zai iya dani kinga ni ban wuri nahuce idan nafito nabaki labari”

KULU! KULU! KULU!!!......
Kira ya doki kunnenta,juyowar dazatai sukai ido hud’u da abba yana mata kallon tuhuma,waige-waige ta farayi nan ta lura ashe tini Hafsa ta gudu ta barta.
”Abba sannu da dawowa”
D’aga mata hannu yayi tare da fad’in,

”Kulu tinba yauba ina lura dake kaf mutanen gidannan ba wanda yatab’a zuwa wajannan saike,abaya na rabu dakene saboda wani tinani da nayi,amma yanzu na kura so kike ki tona min asiri to wallahi tallahi kinji na rantse miki koda wasa kika kuskura qafarki ta taka d’akinnan to dagaranar kitabbata na tsine mikj albarka na tsameki acikin ’ya’yana,kuma kisani ayanzuma idan wani yyaji wannan zancan to banyafe mikiba............✍️

Tsokaci kad’an daga cikin labarin 🏡A WANI GIDA🏡
’YAR GATAN MAMA✍️More comments more typing🥰
🏡A WANI GIDA🏡

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)**_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

__________________________________________________
_________________________


🅿️2️⃣


Na sadaukar da wannan page din gaduk wanda ya karantashi😍😍

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Kuma wannan maganar da mukayi dake yanzu idan kika bari wani yaji tom banya miki ba! nace banyafe miki ba, kulu inamai tabbatar miki zan iya yin komai dan naga na rufe wannan 6oyayyen sirrin nawa, Hauwa kulu kitina nifa mahaifinki ne idan baki rufamin asiriba wazaki rufawa? Dan girman Allah ’yata kibarwa cikin ki”
Abba ya qarasa fad’a yana mai had’a hannuwansa alamar roqo.
”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”abinda kulu taita maimaitawa kenan akan le66enta cike da tsoro, firgici, razani, fad’uwar gaba wanda suka ziyarceta lokaci guda, Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ta sake fad’a tare da dafe qirjinta sanadin bugawar da taji yanayi, Menene Abba yake 6oyewa?
Abba zai tsinemin?
Ya salam..! ta fad’a dukda haka hannunta yanakan qirjinta jitake gaba d’aya kamar qafarta bazata iya d’aukan gangar jikinta ba, Menene Abba? menene? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un tasake fad’a da qarfi akaro na ba adadi tare da d’ago da kanta sama, amma me? babu Abba babu dalilinsa ganin haka yasa tafara jan qafarta cike da rauni tafara takawa da niyyar tabar wajan.
Durqushewa qasa tayi da sauri sakamakon zugi, rad’ad’i da zafin da taji aqafarta, da sauri ta kalli qafar tare da riqewa bakin qofar wani d’aki dake kusa da ita taja jiki ta zauna inda idanunta ke zubar da ruwa kamar hawayenta zai qare, menene Abba yake iqirarin zai iya cireni acikin yaransa saboda shi?
Wannan wane irin sirri ne haka mai girma?
Ohhh!!! Ya rabbi ya rabb!!. abinda take nanatawa kenan ita ba zafin kwalbar data shigetane yake damunta ba A’a wannan sirrin na Abba shi ne yake damunta, wannan wane sirri ne da har Abba yake roqonta akansa?
Azaba ce ta isheta inda tasa hannu tare da rintse idanu tafara qoqarin cire kwalbar data shige cikin tafin qafarta, fad’in zafin da takeji yafi qarfin afad’eshi saboda yau jitake aduniya ba wanda yakaita jin zafi azuciyarta.
Bayan ta cirene taci gaba da tinanin sirrin da Abba yake 6oyewa dukda jinin dake zuba aqafarta bai d’aga mata hankali kamar yadda wannan sirri ya d’aga mata hankaliba.
~~~~~~~~~~
Hafsa ce taji shirun yayi yawa tintana jira ta fito harta fara tinanin kodai ba lafiyaba, hakanne yasa taji kozata mutu sai itama taje taga halin da ’yar uwarta take ciki.
Shigarta keda wuya ta iske halin da kulu ke ciki cikeda tsoro ta qarasa gabanta tare da dafa kafad’arta saboda taga yadda tayi nisa acikin tinani, d’an kwalin kanta ta cire inda tadage ta yaga tad’aure mata qafar dashi sannan tace ta dafata suka nufi d’akinsu.
Likitan gidan aka kira yazo ya duba qafar sannan yabata maganin dazata sha daga baya.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Mama ki taimaka mini wallahi da gaske nake maki mama ki taimakeni, ko bazaki temakeni ba? mama mutuwa zanyi ”

Hankali atashe Luba ta farka daga baccin da takeyi tare da kalle-kalle ko zataga Haneef amma me? Bayanan, tashi tayi da sauri ta nufi d’akinsa dan ta tabbatar lafiya lau ta bashshi, sauri-sauri take sakkowa daga benen tana daf da isowa falon qasa kenan fitilar gidan gaba d’aya ta d’auke, waige-waige ra shiga yi kozata ji makunnin fitilar, takai hannunta jikin makunnin kenan taji muryar muryar Haneef yana wani irin ihu me rikitarwa yana neman taimako muryarsa na shashshaqewa,cikeda firgici da tashin hankali mara misaltuwa ta nufi hanyar d’akinnasa dukda duhun dake d’akin wanda ko tafin hannunta bata iya gani, tana daf da shiga d’akin taji muryarsa asaman benenta yana qwala mata kira yana neman temakonta..........

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Nikuwa Nafi yaya zancen yarinyar nan?
Kinsankwa jiya ban iya bacci ba saboda yadda lamarin yarinyar nan ya tsayemin arai?
wallahi Nafi nashiga cikin tashin hankali”
Abba yafad’a yana kallon Hajiya Nafisa.
”Uhummm, Abba ai sedai haquri nima lamarin ya d’agamin hankali wallahi gaba d’aya gigicewa nayi ajiyannan”
”Haba.. Nafisa bafa nanata zance nace kiminba tambayarki abinda yafaru nakeyi”
Abba yasake fad’a da alama ya fara qosawa da zancen.
”Kasan mu mata ba kasafai muka fiye haquri da mazajenmu ba, itama haka taje taita wauta shi ne fa jiyan yace tazo gida zaizo to daga bayama saiya turo mata saqo yace wai tayi zamanta ya yanke alaqar auren dake tsakaninsu ”
Innalillahi Abba yaita ja kafin yace akira masa ita, Hajiya Nafisa da kanta ta tashi taje tayo kiranta .
”Ke...... Safiyya fad’amin menene ya had’aki da Mukhtar har ya sakeki? ko bakiji abinda nace bane? ”
Abba yafad’a cikin d’aga murya kamar zai rufeta da duka.
”Abba wallahi ba laifina bane ba shi ne da laifi ”
”bazaki fadaba kenan sai jikinki ya gayamiki ko”
Ya qara fad’i yana huci kamar wani zaki.
”Abba banso zan fad’a ba amma tinda kadage zan fad’ama, Abba tinda aka kaini gidan mukhtar kullum idan dare yayi akwai wani d’aki da tinda naje gidan baitab’a bari na shigaba, shi ne rannan nad’auki makullin d’akin bai saniba bayan yafita naje zan bud’e saigashi ya dawo yana ganina awajan shi ne fa yace wai na tawo gida zaizo gidan daganan kuma yace wai ya sakeni... ”
Ta qarasa fad’a tare da sakin kuka mecin zuciya.
”Tom naji Allah yasa hakan yazama alkairi ”Abba yafad’a yana ficewa yabarsu ad’akin, gani. haka yasa itama Safiyya tashi ta koma d’akinta na gidan.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Cikeda qololuwar tashin hankali Luba ta koma hanyar benen da niyyar tahau saikuma taga fitilara gidan tafara farfari atake wasu daga cikin qwayayen suka fara farfashewa fankokin d’akin suka d’auki wani irin qara kai sekace qarfe akasa ana bugunsu, toshe kunnuwanta tayi tare da sakin wata razananniyar qara tana mai rintse idanuwanta, idonta arufe tafara taka matattakalar da gudu-gudu saboda yanda takejin kukan Haneef ya qaruwa jitayi tana taka ruwa aqafarta mai danko bud’e idonta tayi domin taga menene awajan dukda tasan bazata gani ba sanadin duhun daya mamaye wajan gaba d’aya, amma me? ga mamakinta saita ga haske kamar duhu baitab’a zuwa wajan ba, wata razananniyar qara ta saki tare da toshe bakinta take qafarta ta fara rawa jikinta ya fara karkarwa inda ta sake ware idanunta dan ta tabbatar da abinda take gani............


’YAR GATAN MAMA✍️


More comments more typing🥰

*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)**_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

TUNATARWA!!!

LOKACI WANI ABUNE DA BABU ABINDA YAKAISHI GIRMA ACIKIN RAYUWAR DUNIYA BAKI D’AYA, DAN HAKA MU RIBACI LOKACINMU TIN KAFIN YA KUFCE MANA, ALLAH YASA MUDACE YARABAMU DA IYAYENMU LAFIYA👏.

🅿️3️⃣


Wata razananniyar qara ta saki tare da toshe kunnuwanta take qafarta ta fara rawa jikinta ya fara karkarwa inda ta sake ware idanuwanta danta tabbatar da abinda take gani... me zata gani?, Jini ne ke tawowa jikin matattakalar benen sai kace ana yanka raguna, duhu-duhu ta fara gani inda jiri ya fara d’ibarta kanta kuwa jitayi kamar and’ora mata dala da goron dutse tsabar nauyin da yayi mata, Jitai gaba d’aya d’akin yana juya mata kamar wadda tahau kumbo takasa koda motsi balle ta qarasa tahau saman tashin hankalinta ne ya qaru sanda ta lura jinin qara yawa yakeyi tamkar wanda ake zuboshi dafe kanta tayi tare da sakin qara mai qarfi ta fad’i awajan.
~~~~~~~~
”Hafsa!, nifa kamar qara nakeji abangarensu Haneef ”Kulu ta fad’a tana sauka daga kan gadon, ”A’a Hauwa kema kinsani sanin kankine bayau kika farajin iface-iface agidannan ba balle kitada hankalinki , kinga ni saida safe”Hafsa tafad’a tana gyara kwanciyarta.
”Haba Hafsa Mama Luba ce fa take qara kumama muryar ba tatabace itakad’ai, kai... wallahi nidai kozan mutu sainaje naga ko lafiya”tafad’a tana fita daga d’akin.
~~~~~~~~~
Gudu-gudu sauri-sauri ta sakko daga samansu ta fice daga bangarensu, Saurin da takeyi ne yai sanadin tsinkewar takalmin qafarta batai wata-wataba ta sunkuya zata d’auka amma me saita nemi takalmin ta rasa nan da nan ta kalli d’ayar qafartata amma saitaga warin aqafarta d’aya kuma babu, addu’a ta bud’e baki da niyyar tayi taji bakinta yayi mata nauyi, cikin qarfin hali da dakewar zuciya tad’ago domin taci gaba da tafiya kawai saitaga wasu mata sun giftata da sauri suna sanye da jajayen riguna ajinkinsu hannayensu na d’auke da wani abu wanda ta kasa tabbatar da menene, tom suwaye wad’annan?, menene ahannunsu?, ina kuma zasuje?, ta tambayi kanta tare da qara saurin tafiyarta da niyyar saita bisu taga ina zasuje kuma taga suwane ita sam tama manta da abinda yafito da ita da tsohon darennan.
Tafiya sukeyi tana binsu gashi sam sunqi su waigo koda sau d’ayane, Batare da tsoro ko tinanin wani abu zai iya samuntaba ta rinqa binsu, tafiya suke kamar wad’anda zasu bar gari batai auneba sai ganinsu tayi awani wawakeken daji mai matuqar duhu tare da manyan bishiyu bata iya ganin komai giftawarsu tsayawa tayi tana kalle-kalle lokacin data nemesu ta rasa sun 6ace mata 6at ko wulqawarsu bata gani tana cikin dube-dube idonta yakai kan wani wawakeken kogo me babbar qofa kuma tana hango haske jajir acikinsa, batare da wani tinaniba taji lallai saita shiga wannan kogon taga menene aciki, wata irin wutace keci gungu guda kamar wutar daza’a dafa mutane acikinta banda iface-iface babu abinda kunnuwanta keji , tsoro bai kamataba saida taga mutane suna wucewa d’aya bayan d’aya kuma da alamun dukkanninsu mata ne kowacce idanunta tamkar gwarwashi saboda ja baka iya gane fuskokinsu dan duk wadda ta wuce saidai kaga fuskarta baqiqqirin jan idanunta kad’ai kaje hangowa, hankalin kulu ne ya tashi amma hakan bai hanata qara zura jiki cikin kogonba bakinta d’auke da addu’a wadda sai ayanzu bakinta ya iya karantawa, tintana leqawa ahankali abu har ya kaita ga ta shige cikin kogon, wata macece mai matuqar qiba da tsayi ta tawo zata wuce daf da inda kulu ke tsaye tana saqe-saqe niyyarta idan matar zata wuceta tasa hannu tacizge baqin qallen dake fuskarta, batare dataga zuwan matar guntaba kawai saiji tayi taja hannunta ta qarfin tsiya tayi-tayi ta qwace amma matar tafi qarfinta janta take iya qarfinta suna tafiya batare data waigoba hai saida.....


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Lallaima Mukhtar ya d’auko ruwan dafa kansa harni zai sakarwa yarinya saboda tana qoqarin ganin wani banzan sirrinsa wanda bashi da ma’ana?, nikam indai na amsa sunana NAFISATU to wallahi ni da kaina saina binciko wannan sirrinnasa ”, hajiya Nafi ke fad’a bayan Safiyya ta tashi daga haka itama tashi tayi tad’au abinci tahau ci cikeda saqe-saqe harta gama ci. Bayan tagama cine ta shirya domin zuwa unguwa wanda daman shi ne shirinta ayau Abba yazo ya tsayar da ita.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Abbane a 6angarensa abubuwa da dama sunbi sun cikamai qwaqwalwa ba abinda yafi d’agamai hankali illah tinanin yadda akai Kulu tasan yana da d’akin sirri kuma hartake qoqarin sanin mene awannan, sannan kuma ga Safiyya ma mukhtar ya saketa saboda wani sirri nasa shima,” kai!... ya fad’a tare da dafe kansa da hannunsa zumbur yayi ya miqe tare da buga hannun kujera da qarfi yana huci yace kai..!! bazai yuwuba dolene nima na binkici wani sirri ne da mukhtar dahar yasakomin yarinya akansa.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda Luba ta fad’i ba ita ta tashiba harsaida safiya ta fara sannan gari ya fara haske, jitayi ana jijjigata ana magana, damqe idanunta tayi taqi ta bud’e dan atinaninta wani sabon tashin hankalin zata gani idan ta bud’e idon, baigajiba haka yaci gaba dayimata magana yana jijjigata kamar me tashin yarinya daga bacci.
”Mama dan Allah kitashi, kitashi nace! safiya fa tayi tin asuba na fito naganki anan na tasheki kikaqi tashi har ruwa nazubamiki kikaqi tashi mama kitashi”
Haneef keta mata magana amma dukda haka taqi bud’e idon dan har yanzu tsoro bai bartaba gani take kamar Haneef d’inta ya mutu wanine yazo cutar da ita yakemata tamkar haneef d’inta.
Larai mai aikinta ce ta shigo zata fara gyare-gyaren wajen taga Haneef durqushe gaban Luba yana mata magana taqi tashi, aikuwa arud’e Larai ta qaraso tana fad’in, ”Haneef ! Haneef!! mene yasamu hajiyan anan? Haneef magana nakema kayi shiru kana kuka”ai Luba bata bari Haneef yaba Larai amsaba tai maza ta bud’e idonta tare dasa hannu ta janyoshi jikinta tana sakin kuka mai cin rai.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda tafara janta bata saketa ba harseda ta kawo ta inda zai sadata da d’akinsu sannan ta saketa tare da buge mata qafafuwa tai wucewarta tafice, Hankalin kulu atashe taja jiki tayi d’akinsu jikinta duk yabi yayi tsami kamar wadda tayi gasar tsere ko dambe amma duk da haka ba jikinnatane ya dametaba, itayau abubuwa sun qara dagukemata ga maganar sirrin Abba da taso gani batai nasaraba, gashi tafita atsohon dare taje inda bata saniba towai ita mema yafitar da ita? ta tambayi kanta, ”Au ashefa d’akin mama Luba nafita zuwa ”taba kanta amsa take kanta yakuma sarawa saikuma tai zumbur ta miqe cike da qwarin gwiwa tai hanyar....
’YAR GATAN MAMA✍️.More comment More typing😍.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)**_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


Assalamu alikum 🤝.
Ina gaida kowa tare da yi masa fatan alkairi😍. Duk naga saqonku gareni kuma nagode da soyayyar da kukanunamini Allah yabar zumunci ameen. Dalilin dayasa jiya baku jiniba kuyi haquri MURA ce taimin kamun kazar kuku ciwon kai bazai barni nayi typing ba, dan Allah ina barar addu’arku gareni Allah yabani lafiya yasa nagama wannan labari lafiya👏.


🅿️4️⃣.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Zumbur tayi ta miqe tare dayin haryar da take tinanin ita tabi hartakaita ga inda taga wannan matan, tsayawa tayi tana tinani bansan meta tinaba sai ganinta nayi tajuyo tayi d’akinsu, shigarta keda wuya taji ana kiraye-kirayen sallar asuba niyyarta tad’an kwanta ta rage nauyin jikinta to ashe lokacin sallah yayi, haka dai taita saqe-saqenta hartaje tayo alwala tazo ta tada sallar bayan ta idarne taiwa kanta gata wajan d’aukar Al’azkar tafara zikirin safiya bayan tagama kuma ta d’auki carbi takama istigfari kafin ta gama kam gari ya waye kowa yafara safgarsa, tashi tayi domin taje tagaida Abba da Hajiya Nafi da kuma Mama Luba , Wanka tashiga tayi sannan tazauna tana shiryawa. Sallama taji anyi abakin Qofa, amsawa tayi tare da tashi tana ”aunty Safiyya da kanki idan nemanmu kike aisaiki kiramu ko”
Tafad’a tana kallon Safiyya fuskarta d’auke da qayataccen murmushi.
”A ’a Hauwa aini nake nemanki baidace ace nakiraki ba gwara na taso nazo da kaina saikinfi d’aukar abin da muhimmanci”
”Ah! haba aunty Safiyya aikin isa danine dahar zakiyi kirana, kuma dama inada niyyar nazo gunki idan nagaida Abba dasu Mama ”
”Hakan yayi kyau to gama shiryawa sai muje tare mugaishesu koba hakaba? Hakane. Ta bata amsa tare da d’aukar hijab d’inta suka fita su biyu saboda Hafsa bata tashi daga bacci ba da ciwon kai takwana jiya.

Sallama sukai 6angaren Hajiya Nafi suka shiga suka gaisheta suntarar da ita tana karyawa dan haka basu wani dad’eba suka fito sukai 6angaren Abbah.
Shigarsu keda wuya suka taddashi yana falon atsaye hannunsa nannad’e abayansa yanata zagayen falon da alamu dai hankalinsa atashe yake.
”Salamu alaikum”
Suka had’a baki yin sallama tare d kutsa kai ciki, shiru Abba bai amsaba da alamama baisan suna yiba.
”Salamu alaikum”Suka sake fad’a akaro na biyu amma bata canza zaniba dan yanzunma bai amsaba, kallon juna sukai atare sakamakon zancen zucin Abba daya fito fili sukaji.
”Ni yanzu ta ina zanfara ne? Hauwa-kulu d’iyata ta cikina na qoqarin tonamin asiri dukda na dakatar da ita amma nasan bazata dakata ba saboda tad’auko taurin kai irin nawa, Ga mukhtar mijin Safiyya na qoqarin tozartani, tsorona kar Safiyya da Kulu su had’a kai wajan yaqata”
Abbane ya fad’a danshi baisan akwai wasu awajanba dan ba qaramin nisa yayi atinani ba, Firgita yayi tare da d’anyin baya kad’an yana murza idonshi danshi tinaninsa amafarki yagansu ba gaskeba, tsoro ne qarara ya bayyana akan fuskarsa kafin yai sauri yadawo da nutsuwarsa ya kallesu d’ai-d’ai sannan ya samu waje ya zauna yana tambayasu.
”amm... nikam tun yaushe kuka shigo nan? ”yai tambayar har sannan da alamun tsoro ashinfid’e akan fuskarsa.
Kallon juna sukayi tare da had’a baki wajan fad’in, ”Baba yanzu ne muka shigo ”ajiyar zuciyq ya sauke tare da yin sauri wajan miqewa tsaye tare da cewa”Tom ina kwanan ku? ”, abin na Abba kuma yafara basu tsoro haka suka daure suka amsa kafin suyi wata maganar yaishigewarsa ciki ya barsu anan dan duk baisan abud’e yabar d’akinba dan baya buqatar kowa yanzun, Jiki asanyaye suka tashi sukafita daga d’akin sukayi haryar da zata sadasu da sashen Mama Luba, Ga mamakin Kulu sanda suka shiga saitaga bataga alamun jiya anyi tashin hankali awajanba, ”Tom amma ihun me mama Luba keyi tsakiyar dare? ”ta tambayi kanta, suna niyyar tambayar Larai nai aikinta kenan sukaga Haneef ya sakko yana ”Aunty Kulu Mama bata da lafiya sun kusa sukashemin ita jiya da daddare yanzuma sunce bazasu bartaba saisun kasheta ”
”Suwaye zasu kashe ta? ”
Suka had’a baki wajan tambayarsa, bai iya

Please Login or Register in order to submit comment