Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBEYou Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

[7/22, 1:08 PM] Sis Asma: BISMILLAH
Copy by ZAINAB BUTALAWA

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🍱🍱🍱
JIN DADI SABO


1


Official
By
AsmaBaffa
ALHMDLLH ina Godiya ga Allah da ya bani damar sake rubuta sabon Novel dina JIN DADI SABO. kamar yanda muka fara lfy Allah yasa mu gama lfy tare da masu karatu baki daya.

Ina godiya gareku fans dina makaranta novels dina yan groups.

Jinjina ga masu sharhi kunfi kowa birgeni wlh yanda kuke karantawa kuna bibiyar novels tun daga farko har karshe,ina addua Allah yasa mu Karu da juna, ina fata Allah yasa novel din yayi muku sweet ya fadakar ya kuma nishadantar Ameen.

Masu korafi musamman Wanda basa tsayawa su fara karatu daga farko kawai wajen dadi suke karantawa basu San ma ya novel din yake ba amma kuma akwai kawo korafi sai ka ganar dasu suce ai ba daga farko suka fara ba, Dan Allah inhar ba daga farko kika fara ba karki kawo korafi Sabo da korafi bazai karbu ba😅.nafi son masu bibiya filla filla.

Wajen reply na Sharhi fans a dan kara hakuri ko da zaku ga banyi reply ba ko banga na wata ba na tsallake ayi min afwa,da masu magana ta Pc,masu kira etc duk muyi hakuri da juna pls Sabo da dole sai anyiwa wasu ba dai dai ba.

Idan kunga wani abu da bai dace ba zaku iya gyara min fans tunda dole a kwai kuskuren da masu karatu kadai ne suke ganowa, Sharhi shi ke sawa novel ya tafi dai dai yanda ake so.

Duk wani tnx bana sonsa idan nayi posting a daina rubuta min tnx ko haka👍duk masu tnx bazan musu reply ba,masu sharhi zanyiwa😅.

Ban yarda ayi min Poster na Novel ba, a daina kwatanta min Stars dina ana sa pics.

Sharhi kawai nake bukata banda tnx etc.Wannan Page din nakune Gaba daya masoyana makaranta Novels dina daku zan fara sabo da kune masu muhimmanci a wajena.


Birnin tarayya Abuja cikin wani katafaren makeken gida na gani na nunawa a Tv, gidane Wanda ya amsa sunansa babu abinda babu cikinsa,ga motoci maka maka iya shan kallonka babu ta kasa da million Goma, Cikin wakeken palon me dauke da kujeru yan gaske ko a gidan shugaban kasa sai haka, wata dattijuwa ce kyakyawa chocolate color amma mai duhu da ganinta kasan hutu, Naira da Jin dadi ya samu gindin zama a jikinta,Kwalliya da iya shiga ta zauna a jikinta hannunta rike da kafceciyar waya tana latsawa tana Jan tsaki kadan tare da karawa a kunnenta,ba sai an fada ba kasan wannan matar gogaggiyar yar boko ce,Cikin murya me dauke da fada tace Alklsm yaushe zaka dawo ne AHLEEF ? Ya kamata kazo ka karbi aikinka kasan na gaji ka bar min komai a hannuna daga cewa zaka je Saudiya da Paris hutawa har yanzu kaki dawowa,Abbanku baya kasar ka Sani, su Suhail kasan basa nan suna US Schl dinsu ba ayi hutu ba, ni kadai ce aikin yayi min yawa ya kamata ka dawo kaci Gaba da rike dukiyarka tafi karfina.

Dariya Ahleef yayi kadan a waya yace Momee zan dawo soon kiyi hakuri,Better cewar Momee gashi Niima ta gama University yanzu kaga sai mu fara shirin bikinku Ko ? Jin an ambaci matar daya fi so a duniya Niima yaji wani farin ciki a ransa ya kusa mallakar Niimarsa wacce yake ganin tafi ko wacce mace a duniya,duk mata mazaje ne a wajensa Sabo da Niima wacce kullum sai sunyi waya yaji muryarta yake iya bacci,Momee ko dan shirin biki ai dole na dawo am sorry Mum,Murmushi ta saki a rayuwarta babu Wanda take kauna sama da Ahleef ko yayanta da ta haifa Bata sonsu kamar yanda take son Ahleef a duniya.
Bayan sun gama waya da Ahleef cewar Next wk zai dawo gida.

Wata yar kyakyawace Chocolate me kyan diri zata kai 25yrs ta shigo Palon Momee tana faman yatsina fuska,sanye take Cikin wasu Arabian wears dark blue riga da skert masu tsada da kyau jakarta ta ajiye gefe tare da zama kusa da Momee,Momee na gaji yau nasha aiki a Office ga Meeting da mukayi sun kai kala uku,Cike da tausayi Momee tace sannu Niima ai haka aikin yake ba sauki,je kiyi wanka kici abinci sai ki samu ki huta Ko, Da sauri ta Mike ta nufi sama abinta,Yar karamar yarinyace ta shigo sanye cikin Uniform na Islamiyya Zata kai 15yrs tun daga waje take cewa Momee na dawo,yar fara ce yarinyar amma ba kar ba tana da dan Duhu kadan amma ba baka bace, Last Born Latifa kenan cewar Momee wuce ki cire Uniform ki kaiwa me muku wanki a wanke,Yess Momee ta wuce da gudu.

Bayan sati guda da zancen Ahleef zai dawo daga Paris Sabo da dokin auren Niima bai canja Date ba,yau Saturday yaune kuma suka tashi da girke girken tarbar babban bakonsu,Niima dai tana Murna itama sosai dan tayi missing kyakyawan saurayinta.

2pm jirginsu ya sauka a Abuja,Momee ce kawai taje tarboshi tace ita kadai zata je, Tare da escort suka jera motoci guda Takwas.
Janye da Trolley dinsa ya fito,Gaba daya kallo ya koma kansa mata da maza Sabo da tsananin kyawunsa hade da iya shiga,ya tsaru iya tsaruwa,Sumarsa kadai abin kallo ce da birgewa,dan gemun nan tare da dan saje kadan sai sheki sukeyi suna walwali,Fatarsa kadai abin birgewa ce sai ka rantse yanzu aka fito dashi daga cikin engine,ba sai an fadama ba kasan Naira da Hutu tare da Jin dadi Sun ratsashi,sanye yake Cikin kana nan kaya White and Grey color kamshin dadinsa gaba daya ya mamaye Airport din, Dogo ne Amma ba can ba, shi ba me kiba ba sannan ba siriri ba, idonsa dara dara suna lumshewa, fuskarsa tana da dan tsayi kuma tana da dan fadi normal, hancinsa dogo dan lcib baiyi tsini da yawa ba,bakinsa dan karami jajir dashi yana shining,Fatarsa fara ce amma ba irin kal kal ba,wata iri ce ta birgewa shi ba farin dan Africa ba, ba na larabawa ba kuma na bature ba,haka sumarsa ma take Unique ce kamar ruwa biyu haka yake,babu Wanda zai ganshi bai kara kallonshi ba ko maza ne bare mata,tafiyarsa kamar basarake ta maza masu ji da kansu sai shegen Iyayi a cikinsa da gani ba sai an fada ma ba, bazai wuce 31yrs ba yana ji da kuruciya a cikin lokacinsa yake,tun Kafin ya karasa Momee take zuba murmushin Jin dadi danta da tafi so fiye da yayanta na cikinta ya dawo kusa da ita,da sauri ya karaso tare da rungume Momee yana murna itama haka,Cike da ladabi ya gaisheta sai shagwaba yake mata yana narke mata gwanin sha'awa itama tana lallabashi.Momee tace Son lets go nafi so kaci abinci ka huta,cikin muryarsa me dadin gaske me tafiya da zuciyar yan mata cike da iyayi yace Sorry Mum muje,da kansa ya bude mata ta shiga shi kuma Escort suka bude masa ya zauna gefen Momee,suna gaishe shi yana amsa musu da sakin fuska ba wulakanci,Direct gida suka wuce,Latifa da Niima kawai fadawa sukayi jikinsa suna ta tsalle da murna,da kyar momee ta koresu daga jikinsa,shima da yake Shu'umi ne sai ya jawo budurwa r tasa Niima ya rungume kam a jikinsa,ba karamin kyau tayi masa ba,ga wani kamshi da takeyi,Yaji Albarkatun kirjinta male male bisa kirjinsa lokacin Momee ta shiga kitchen,ya wani lumshe ido yace uhmmmmm wannan mene haka kamar jinjirin mage Sabo da laushi,itama Niima tace dashen Allah kenan ni kaina ina ji dasu,dariya yayi ba karamin kyau dariyar tayi masa ba kamar kar ya daina,hakoransa kanana jere suka bayya,yace to maza San min kafin Momee ta fito yana wani shagwaba,Zatayi magana kenan sai Ji sukayi Momee tace ku kuma mene haka? Ban son iskanci ku kiyayeni fa, da sauri Niima ta gudu Bedroom dinta,shi kuma yace Momee Bari nayi wanka nazo naci me dadi kinsan I missed ur food.

Asalin Ahleef
ALHAJI AHMAD SALEES(ALHJ AMADU) Dan asalin kasar Niger ne,tun asalinsu kaf danginsu talakawa futuk, Amadu shi kadai iyayensa suka haifa a duniya, Bayan Amadu ya cika 25yrs iyayensa suka rasu Gaba daya sakamakon hatsarin mota sai yan uwa dangi,sanadin talauci yasa kusan zumuncin ma ba ayi da juna kowa yana bige bigen neman kudi,Amadu duk yafi su zumunci da hakuri tare da tawakali gashi da addini,hakan noma kawai yake danyi dashi yake ci yake sha,watarana yana gona ya hadu da SAUDAT wacce a yanzu take Hajiya Saudatu, yar asalin larabawan libiyace kyakyawa ce ta gasken gaske,fada ne na yan taadda ya barke a kasar tasu sukayi gudun Hijira zuwa Niger,Saudat kaf danginta an kashesu a yakin da akayi a kasarsu ita kadai ce ta tsira ta shige cikin Yan Hijira zuwa Niger,tunda tazo Niger take cikin gari a titi sai wanke wanke da shara da takeyi a wani gida ana biyanta,da haka take rufawa kanta asiri tana wannan gantalin Allah ya hada ta da Amadu a Gona,nan yaji sonta ya kamashi har ya kai ga yi mata magana,tas ta bashi labarinta na rayuwa kuma ya tausaya mata,tun daga ranar suka fara soyayya kullum suna haduwa a gona.

watansu biyu da haduwa ya sanarwa danginsa ya samu mata,sune suka tallafa akayi masa komai cikin talauci sosai akayi bikin,yan unguwar haka suka dinga surutu Amadu ya auri balarabiya yar gudun hijira ba a San asalinta ba etc,cikin bakin talauci na karshe suke Zaune lfy sai uwar soyayya da suke zubawa.
Sun kwashe kimanin shekaru goma sha biyar tare amma basu samu haihuwa ba, tun suna sa rai har suka hakura gashi basu da kudin zuwa asibiti ko maganin gargajiya haka suke ta addua.
Saudat sarkin hakuri, watarana tana zaune makociyarsu ta shigo tare da kawo mata Maganin sanyi Infection na gargajiya, tace Saudatu ga maganin sanyi ba a son mace ta zauna Bata shan maganin sanyi lokaci zuwa lokaci,Godiya tayi tare da karba,wata uku tayi tana amfani da maganin cikin ikon Allah sai ga Saudat da ciki murna ba a magana,har cikin ya cika wata tara ta haifi danta namiji kato kyakyawan gaske ajin karshe,ko ina zuwa akeyi kallon jaririn Sabo da kyansa,ranar suna yaro yaci suna Ahleef,Ko hakikar suna ba a yanka masa ba Sabo da talauci,bayan wata uku da haihuwa talauci ya kara zurfafa musu sai kawai sukayi shawara cewar gwara su koma Nigeria da zama garin kasuwanci ko Allah zai sa su samu aikin yi,basu tsaya ko ina ba sai Nigeria Cikin Kaduna state.

Cikin ikon Allah wani hamshakin me kudi ya dauki Amadu gadi a bakin gate tare da bashi daki da toilet a gidan yace ya kawo iyalinsa su zauna tare,Zama yayi zama Sun kusa shekara lokacin watan Ahleef bakwai Me kudin ya biyawa Saudatu da Amadu aikin hajji tare da jaririnsu,sannan ya siya musu katon rago aka yankawa jariri Ahleef na Hakika, bayan sun Dawo da wata biyu lokacin Ahleef ya cika 1yrs Allah yayiwa me gidan da suke aiki rasuwa,bayan rabon gado gidan ya tarwatse Gaba daya yaran Alhaji suka koresu gida ya zama na gado, Shine silar barin gidan gaba daya basu San inda suka nufa ba,ruwa,iska,rana sanyi duk ya kare a kansu har Allah yasa wani mutumi ya gansu ya tausaya ya basu wani dan karamin daki dake a kofar gida kamar na maza,anan suka raba suna zama, Ahj Amadu ya koma dako a kasuwa ita kuma tana wanki da guga.

watarana ta bar Ahleef a Daki ta shiga wani gida karbo ashana zata hura wuta a waje ma suke girki kowa a titi yana kallonsu,kuma bandaki daya suke shiga da wasu kartin maza samari hakan ma tausaya musu sukayi ganin basu da inda zasu shiga idan shiga bayi ya kamasu,Allah yasa Saudat me tsananin tsafta ce kullum toilet din samarin a wanke kal ita take wanke musu kuma suna jin dadi.
Tana shiga karbo ashana ashe wasu samari masu satar yara suna siyarwa matsafa suna fakonta a unguwar su biyu,jira dama suke su samu dama, Ranar ba kowa a layin kawai suka fada dakin tare da fesawa yaron Powder ta bacci suka sakashi cikin towel tare da fita da gudu suka fada motarsu sai birnin tarayya Abuja dama abinda ya kawosu Unguwar kenan.
Saudat tana fitowa neman duniya Bata ga Ahleef ba haka ta haukace Ko ina tana tambaya mutane Sun tausaya mata,Shi kanshi Amadu Kuka wiwi ya dinga yi da yaji cewar dansa da suka fi so a duniya an sace shi, Kullum cikin kunci suke gashi Saudat ta nace ita tasan danta yana raye,kuma idan an sace yara Kudu ake kaisu dan haka ita wai dole sai Sun bar arewa,haka ya lallabata ta hakura har suka kara samun wani ya dauki Amadu yake kula da flowers na gidansa,part guda ya basu suke zama lfy, har suka kwashe shekaru ashirin da biyar a gidan,Sai me gidan ya fara neman Saudatu yana so yayi lalata da ita ganinta kyakyawar gaske tafi matarsa,Amadu yana Jin labari ba yanda Amadu ya iya haka ya kwashi matarsa har zuwa Abuja City, Cikin sa'a kwanansu uku da zuwa suka samu wani attajiri Alhaji Dauda ya daukesu aikin gadi a gidansa, ita kuma Saudat zata dinga yiwa yaransu wanki, kaf iyalan Alhaji Dauda basu da tarbiya bare mutunci,shi kadai ne me dama dama, boysquaters ya basu a nan suke zaune,cin mutunci iri iri ake musu a gidan haka suke hakuri,ganin haka yasa Saudat ta fara Soya doya da kwai a bakin wata yar kasuwa kusa da wani katon mall na kece raini,Idan tayi wankin da takeyi da yamma sai ta tafi wajen sana'ar soya doyarta,dake ta iya sai take samun kudi sosai har masu kudi suna tsayawa su siya Sabo da tayi mugun iyawa kalarta daban ce kowa yaci sai ya kara,ta tsare mutuncinta normal.

Rayuwa kullum ja take dake dama basu samu haihuwa da wuri ba,Har aka kwashe shekaru 5yrs yanzu kenan yayinda Idan An hada da shekarun tun haihuwar Ahleef shekaru 31 kenan,har yau dansu Ahleef na ransu suna fatan ganinsa nan gaba, yanzu Idan kaga Ahleef kaga iyayensa baza kace su suka haifeshi ba, Sabo da Sun tsunfa Sun manyanta sai ka rantse kakaninsa ne tunda dama sai da suka manyanta sannan suka samu haihuwa,gasu kuma kullum a wahala suke da gwagwarmayar rayuwa shiko Ahleef yana cikin daula.

Bayan barayin Sun sace Ahleef suna ta sheka gudu a hanyar Abuja sojoji suna tsaida motoci ana dubawa Cikin sa'a aka kamasu tare da fito dasu su biyu daga motar,jaririn yana hannunsu suka fara dukan barayi tare da tambaya ina suka samoshi,Daya cikinsu sojojin yana rubuta komai a littafi,Cikin barayin suka ce wlh satoshi mukayi dama sana'ar muce mu Sato yara muna siyarwa da Matsafa, Wannan yaron ma sunansa Ahleef mun dade muna bibiyarsu har muka samu nasara,sunan yaron Ahleef min San iyayensa....kafin y'a karasa daya abokin satarsa ya rada masa Mu gudu fa daji,ba tare da tunani ba suka arce da uban gudu da niyyar su boye a daji,Sojoji suka fara Harbinsu ta ko ina nan take duk suka zube kasa matattu.
Bayan komai ya kammala suka dauki Jariri da sa hannun Gomnati aka fara cigiyar iyayensa a kafafe na Media Amma ba a dace ba yaro Ahleef har ya kwashe 1mnth a gidan raino.

Abba Alhaji Sulaiman Yahaya da Matarsa Hajiya Amina Momee Asalin yan Nasarawa lafiya ne gaba daya har Momee danginsu Suna can duk da cewa suna zumunci sosai da danginsu duk da cewa iyayensu Sun rasu tuni dama amma Momee Babanta yana raye can garinsu,suna yawan kai masa ziyara tunda sunyi sunyi ya dawo Abuja yaki.
Momee da Abba mutanen kirki ne masu hakuri ga tausayi,tunda sukayi aure Allah bai basu haihuwa ba har suka kwashe 8yrs haka,shine Momee ta bawa Abba shawara yaron Ahleef da suka gani a tv ana neman iyayensa ba a samu ba ita tana so suje ta karbi rainonsa yaron ya Bata tausayi gashi kuma Allah bai Bata Haihuwa ba, nan Abba ya Amince da sa hannun Gomnati aka basu yaro tunda anyi cigiya a Media iri iri amma Allah bai sa an samu iyayen jariri Ahleef ba.
Su Momee
Cikin so da Gata hade da Amana suka rike Ahleef,Momee bayan Ahleef ya cika shekara 6. Momee ta samu ciki ta haifi yarta Niima kyakyawa,Ahleef lokacin yana primary schl ta masu kudi,bayan 3yrs Momee ta Haifi yan biyu Salman da Suhail,Ahleef secondary schl da university gaba daya a London yayi su, cikin gata ya karanta Harkar kasuwanci har sai da ya gama Masters ya dawo Nigeria,Lokacin Sun shaku da Niima tana University amma a Nigeria tayi,Ita kuma Niima Bata wani son Ahleef Sabo da gani takeyi iyayenta sunfi sonsa kuma ba su suka haifeshi ba, sai take kishi da bakin ciki Sabo da Momee tafi sonsa Abba ma haka,su kuwa su Salman ba ruwansu suna kaunarsa kamar dan uwansu na jini,Dama tun Ahleef yana yaro su Momee basu boye masa ba yasan komai shi ba dansu bane.
Bayan Shekaru masu yawa Momee ta haifi autarta Latifa wacce yanzu take 14 to 15yrs,Ahleef yana gama secondary schl Abba ya bashi jari da Company har biyu kyauta tare da sa hannun lauyoyi da yan uwansa Sabo da halin rayuwa tunda yasan Bashi da gadonsa shi yasa ya bashi tun yana da rai.
yana juya Kudin da kula da Companies Kafin kace me sai ga Allah ya bunkasa abin ya zama Me dukiya na sosai yayi suna a duniya har yafi Daddy ma kudin,suma su Salman suna fara university aka basu nasu harkar,Niima ma haka,Momee ma haka,kowa a gidan da nasa na kansa yake amfani babu Wanda ya dogara da na wani sai Latifa yarinya,Duk gidan yan boko ne Abba kuwa dan Boko ne dan kasuwa kuma dan siyasa Wanda ya rike mukamai da dama manya yanzu haka shine Sakataran Gomnati na kasa baki daya,gidane Na Tarbiya basu da wata matsala har soyayya tayi zafi tsakanin Ahleef da Niima wacce ake tunanin aurensu kwanan nan.
Ahleef Yana da addini ga ilmi,bashi da wata matsala sai watarana yana da raini sama sama,ga Gadara da takama kuma yana fama da iyayi etc bashi da abokin da ya wuce Farhan,Farhan shima namiji ne kyakyawa halayyarsu daya da Ahleef yana da haske amma ba can ba,yafi Ahleef fara'a kawai,tun suna yara tare suka taso iyayensu masu kudi ne suma su Farhan, amma shi Lawyer ne.

ci gaban labari

Ahleef Zaune yake saman 3seater dake katafaren palon Momee suna hira sama sama,sai ga Niima ta shigo a fakaice ta watsawa Ahleef harara tana zaginsa a ranta dan Iska ya gama mallake musu iyaye,har ya zama shine me kudin ma, Inshaallah sai na jefashi a bakin cikin da zai bar gidanmu baki daya shege komai nasa me kyau kamar aljani to wlh duk kyansa bazan ji kaunarsa ba tunda ya mallake mana iyaye sunfi sonsa akan kowa.
Ahleef kuwa bai san ma tanayi ba, sai da Momee tace zauna mana kin tsaya masa a kai kamar me tunani,Ahleef cike da murna, wani sanyi ya mamaye masa zuciya ga Son Niima yana karuwa masa kullum,hannun ta ya jawo zauna yan mata ki huta,sannu,ya Office yana lallabata,ita kam aranta haushi kamar ya kashe ta,a fili kuma sai zuba murmushi takeyi.

Wata kyakyawar Budurwace yar 16yrs fara kwal kwal ga kyau kamar ita tayi kanta,komai nata ya kai karshe,duk inda kake neman kyakyawa ta karshe to kazo wajen wannan yar matashiya,dan lips dinta Pink shine abin birgewa, Girar nan me yawa, ga gashi yalo yalo ya kwanto a gaban goshinta har wani saje ne da ita yabi ta kasan kunnenta kadan,hancinta me kyau amma baiyi tsini da yawa ba,idonta dara dara masu kyau, abinda yafi tafiya da Imanin mutane shine Dirinta kyan sura ga Hips kamar an zana mata shi.
Faduwa tayi a kasa ta saki kuka me karfi tana shure shure da Burburwa,Wata Dattijuwa kyakyawa Ce cikin kidimewa tare da firgici tace Shukura? Budurwar tayi banza da mahaifiyar Tata taci Gaba da kukanta,Shukurata tashi zo ki fada min waye ya taba min ke ? Nan ma Shukura tayi mata banza sai kuka take,sai da tayi kukanta ta koshi sannan ta turo baki cike da shagwaba tace Inna.... Ba...ba.. Aishalle bace take min yanga akan ta siyo Tsire tana ci ni kuma baki bani Kudin na siya ba, Da sauri Inna ta Mike jikinta na rawa kamar uwarta ce tayi magana,Dari biyar ta dauko ta mikawa Shukura gashi maza yi shuru ki siyo kema kice,sai lokacin ta goge hawayenta kamar yarinyar yaye sannan ta saki murmushi tayi waje da sauri.

Misalin 15mnt Shakura ta dawo da tsirenta ta nemi waje can gefen rumfar dake gidan nan ta kwalawa Babatar kira Innaaa.....Inn...kafin ta rufe baki har Inna ta fito tana sauri,Shukura tace cike da Shagwaba Inna yi min fifita,Ba musu Inna ta fara yi mata fifita da mufici tana sannu ci

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

8 months ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment