Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBEYou Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namuAlura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOCMasu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our servicesNote that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame usNote that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download itNote that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTThis Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/2, 9:20 AM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: *🎀AKWAI BAMBAN CI🎀*

_*DAGA ALK'ALAMIN*_

*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*


_*{MAGAJIYAR KAINUWA}*_

*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


_ALBISHIRIN KU MASOYA KARATUN LITTAFIN HAUSA,KAMAR YANDA NASABA KAWOMAKU LITATTAFAN HAUSA MASU MATUL'AR NISHADANTAR DAKU SUKUMA FAD'AKAR DAKU TAREDA WA'AZAN TARWA,TO YAUMA GANI CIKIN WANI K'AYATACCEN LABARI DABAKU TABA JIN NAKAWO MAKU SHIBA,KUBIYONI KUSHA KARATU LFY_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*YA AL,UMMAR MUSULMI INAMANA JAJEN SHIGOWAR WATA SHEKARAR UBANGIJI YAKAREMU DAGA SHARRIN DAKE CIKINTA DA SHARRIN DAKE BAYANTA YAH ALLAH ALKIRIN DAKE CIKI KASADAMU DASHI,KAKAREMU DAGA MAHASSADA DUK MAINUFIN MU DA SHERI ALLAH KAMAYAR MASA DA KAYANSA AMEEEN DON IYAKANA ABUDU*

1/1/2020.


1&2.

*KOTU*

"Yamai girma Mai Shari'a inaso kotu tabani dama zanyiwa Adam tambaya"

"Alkali yace kotu tabaki dama"

Mik'ewa tayi tanufo wajen Wanda ake tuhuma ta na binsa dawani da k'ik'in kallo kamar zata zabgamashi Mari.

Tana kallon tsakar idonsa yayinda idon nasa yayi jawur kamar Jan gauta,

Kauda kanta tayi tafara magana,
"Malam Adam inason ka
gayama kotu tayanda akai kasan cewar za,a kashe Alh mahd"

Duk jijiyoyin kanshi suntashi sunyi rad'o rad'o saboda b'acin rai,

Shiru yayi bai tankaba,
"Malam Adam dakai nake kobakaji tambayar dana ke maka bah"

"Cikin dauriya da danne Abunda ke ransa yace ina kwance agidana da misalin karfe biyu na dare aka turo man text awaya na,cewar idan inason ceton sirikina to intaho yanzu don gashi nan zasu kasheshi,Kuma lokacin ni ina Abuja sukuma suna kano"

"Ban sanar da matata bah saboda bacci take kuma bata da isassar lapia shiyasaka na tashi asace natafi cikin wannan daren, Allah ne yakaini Abuja lafiya,"

"Sadda naje nasamu motarsu akofar gidan don haka sai nabi tawata hanya cansama, direct dakin Alh nanufah saidai sadda zanshiga natarar da Ankasheshe........"


"Kallon banza ta wurga mashi kafin tace taya akai kasan cewar akwai wata hanya gidan, bayan hanyar da kowa yakebi yashiga,sannan suwaye wadannan mutanen dasuka kiraka konace suka maka text din cewa za,a kashe Alh"

Shiru yayi baice komiba don Tabbas yaga Alamar dagaske *MUBINAT* saita tona masa Asirin da dagashi sai ita sukasan hakan,Amma taya zai iya furta wannan A bun gaban mutanen dasuke ganinsa da kima da mutunci,shin mubinat kuwa tayi mashi Adalci kenan idan bata rufa mashi Asiri bah waye zai rufamai,
Saida Sukai alkawarin babu Wanda zaiji bare yagani Amma dan me take kokarin sai kowa yasan halin da yashiga.

"Malam dakai nake kayi shiru kobaka da A bun fad'ane"

Namma shirun yayi don baisan ta ina zaifara bah.

Kenan bakada gaskiya tunda har kayi shiru.

"Cikin da sassar muryansa yace mutanen Abokan aikina nane nadah, sunajin haushina tasilar fita daga cikin kungiyarsu shiyasa suka dauki matakin sakani cikin bala,in da bazan iya fitar dakaina bah"

Wani jakin murmushi tayi tace"munji wannan to kofar dakabi kuma ya akai kasan hanyar bacin ko iyalan dake gidan su basusan da itaba,"

Sadda kanshi kasa yayi bazai iya fadaba,
Taya zai buda baki acikin wad'annan jama,ar dasuka cika kotu cewar suntaba shiga gidan zasuyi fashi, wannan mummunar kalma ce da zata saka duk Wanda yake goyon bayanshi ya daina,

"Yamai girma Mai sharia wannan mutumen babu wata gaskiya tare dashi, munafiki ne shine yakashe man mahaifina mama na takamshi dumu dumu yana cakamashi wuka,"

Ta na maganar ta na zubar da hawayen bakinciki,

"Tacigaba yamai sharia inason kotu data gaggauta yanke mashi hukunci daidai da laipinsa,inason adaukar mana mataki kanshi don barin irinsu yana kawo barazana ga sauran Al,umma"

Tayi godiya godiya takoma tazauna,

Alkali yayi y'an rubuce rubucensa sannan yad'ago "yace ko barrister lawan yanada A bun cewa,"

"Yace Aa ya Mai sharia"

Sake duk'awa yayi yacigaba da rubutunsa yajima sosai sannan ya d'ago yace"kotu tad'age wannan kara da akeyi zuwa 25/10/2015 sannan kafin zama nagaba kotu tana bukatar hujjoji masu karfi da za,agabatar gaban kotu,don haka za,acigaba da tsaron Wanda ake tuhuma har zuwa ranar da za,ak'ara zaman,
Kotu tatashi yabuga wannan gudumar Ana fadan.

KOTU!KOTU!!KOTU!!!

*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*

MAMAN MUHSEEN CE✍🏻

*COMMENT AND SHARE*
[1/2, 5:06 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: *🎀AKWAI BANBAM CI🎀**_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*

_*(MRS BB)*_

_*{MAGAJIYAR KAINUWA}*_


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


2/1/2020.


3&4.

Kowa yatashi anata fita yayin da y'ansanda sukazo suka Kama Adam sukafito dashi, hannunsa sanye da unka.

Duk suna nan waje akafito dashi ansashi mota sukabishi da wani jakin kallo,
Zainab yayar mubeenat tace"Mugu gaba d'aya rayuwarka agidan yari zaka gamata ran mahaifin mu bazai tafi abanza bah"

Cikin bakin cikin irin kalaman da take fad'a mubee tace"Amma dai Anty ganin idona ai yasaka ki yi shiru Amma gabana kike zaginsa kina masa fatan tsiya"

"Cikin fad'a tace nayi mashi kozaki dakeni ne"

"Mamansu tace sababbu yanzu ma cikin mutanen saida halin zakuyi, kuwuce mutai gida sakar karun banza"

Yayansu daya kawosu yadauke su yamaidasu gida, kama jira take su isa taruga d'akinta tafad'a kan gado tahau koke koke,

"Meyasa zakai haka Adam,kayiman adalci kuwa irin soyayyar danake maka kenan, karasa dame zaka sakaman sai kashe man mahaifi bayan kasan irin son damukewa juna,taya ma Zan zuba ido katsira wallahi duk da irin son danake maka bazan tab'a bari kakub'utaba don bazan iya jure ganin Wanda yayi silar barin mahaifina duniya bah shikuma yana zaune lafiya,
Nayi Dana sanin Aurenka Adam kacuceni kazalinceni dama dawata manufa ka auran...... Tafashe da kuka Mai tsuma zuciya.

Tacigaba da cewa "ina sonka ina kaunarka Adam,Amma hakan bazai Hana ni mubeenat nadauki fansar ran mahaifina bah wallahi kaima saika bak'unci lahira bazan kyalekaba......tafad'a cikin tsawa......

*jannat* ce tashigo d'akin tasamu waje tazauna,
Ta na tunanin yi Mata magana don tunda a bun yafaru babu Wanda tacewa uffan don idan ta sake tace wani Abu tata ce zatayi zafi gani zatai ta na goyon Bayan Adam,
Bayan bahaka bane gaskiyace itadai bazata iyaganin gaskiya tayi shiru bah,idan don ta Adam ne wallahi bazatayi bah don yanda yatsaneta itama bata kaunarsa saboda yana son duk abunda mubbe take so haka yana k'in duk Abunda mubbee bataso don yakan linka k'iyayyar fiye data mubee d'in.

Tsawon lokacin dasuka d'auka shida mubeenat suna soyayyar su bata tab'a mashi magana bah haka shima,
Saboda mubee batasonta Baku ma sushiri ko kad'an dasun zauna waje guda saisunyi fada'.

Yanzu ma gani tai bazata iya k'yale ta cikin duhuba dole tayi Mata bayani,
Don duk inda gaskiya take to fah jannat batayi shiru saita tanka komai za,ayi Mata.

Tanada fad'a idan antab'ota tanada hakuri idan bakashiga sabgar taba,

Duk gidan mazan kawai suke hud'd'a ta arziki da ita Amma banda uwar da yan matan,

Saida taga ta rage kukan sannan tace"nikuwa dazan baki shawara kiji danace kiyi handling case d'in nan gawani don kitsira da mutuncinki,Abunda nake nufi kiba wani yacigaba don wallahi za,a samu matsala nagaya maki Mijinki bashine ya aikataba,idan kikaciga da treating case d'in nan ahaka wallahi zaki shiga damuwa,"

"Don Adam zai iya kub'uta idan ya kub'uta dawane ido zaki kallai, shin zaima cigaba da zama dake matsayin matarsa kuwa,saboda zaiga matar daya amunta da ita it ace take tsaye don ganin ankaishi kurkuku,taya zaicigaba da zama dake matsayin matarsa,kiyi tunani nikinsan idan nahango gobara ta na tahowa zanyi iyakar iyawata don ganin nasanar dakai kayi hanzarin kwashe kayanka................


Wata irin bangaza mubee tayiwa jannat cikin fushi da masifa tace"don kutumar ubanki har kin isa, mekika sani akan wannan case d'in har zakizo kina gayaman wasu zantuka nabanza da wofi,
Watau karya zauna dani ke kimaye gurbina ko,nafa gama ganoki murjah tun ina gidan nan kikeson Adam,shine yanzu kike fad'an yarabu dani keki aurai ko"

"Murmushi tayi tace bari kiji mubee, ni mijinki bai isan kallo bah,wallahi koga k'afa akad'aura man shi zankwance baiman bah baya cikin tsarin mazan danakeso, don haka kibar danganta shi dani, kenakewa gata don wallahi kina gaf da tafka babban kuskure....nikinga nayi nan kiyi dawata bada jannat bah"

Tafice tabarta ta na hayagaga ita d'aya.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞

"Adam nayi imanin bazaka kashe Alh bah duk da Abunda yafaru tsakanin ku,Sannan baikamata mubee tayi maka hakaba,itace mutun tafarko daya dace tayarda dakai, Amman tagoyi bayan hakan saboda aganinta case d'inku shizaisaka ka kasheshi,"

"Jibeer na sadak'as da cewar nima kasheni za,ai domin banida hujjar cewar bani bane nakashe shi,hajiya taganni sanda nake kokowar cire masa wukar dake cikinsa,atunaninta alolacin nake cakama Sa ita,sannan shidakashi yasakaman Albarka tare dagayaman inda yakai mahaifina yakuma gayan inda zansamu dukiyarmu,yabani wata wasika yace inbawa mubee, sannan yacika da Kalmar shada,"

"Tunda a bun yafaru mubee takasa tsayawa ma muyi maganar fahimta da ita, kullum tazo nan maganganun b'atanci sune bakinta haka zata tafi ta na Mai gayaman magana, wallahi jaber inason mubee yanda baka tunani, inakuma son karashe rayuwata gaba d'aya da ita,Amman abunda yafaru akotu yau yasaka naji tafita raina inajin ciwon irin yanda tamun nayarda bakowane zai iya rikemaka amana"

Idonsa yayi jawur kamar Jan garwashi saboda b'acin rai,
Yakalli jabeer yace"lawyer na yace idan wannan karon babu wani cigaba gaskiya bazai iyaba,kaga shikenan nitawa takare ko jabeer"

"Taka bata k'areba Adam Allah yana tare damai gaskiya ninagaya maka zaka kub'uta cikin yardar ubangiji,kacigaba dayin Addua idan ma yace bazai tsaya maka bah ni zansan duk yanda nayi don ganin kawanku daga wannan zargin.....

Dan sanda ne yazo yacemasu lokacinsu yayi haka aka tusa Adam gaba akashigar dashi cell.

💞💞💞💞💞💞💞

Gobe me Yakama za,a koma kotu,
Hankalin mubee Yatashi anya kuwa bazata d'auki shawarar jannat bah,bazata iya jure cigaba dayiwa Adam cinfuskar datayi masaba ranar farko,to idan ban tsayawa dady bah wazai tsayamai shin yazanyi ni mubee,bayan babana Zan yi kokuwa bayan mijina..........

*(NIKUWA NACE AMSARKI NAGA MASU KARATU)*

*KUCIGABA DA KASANCEWA DANI FANS YANZU AKAFARA,*

*TAKUCE HAR KULLUM MAMAN MUHSEEN*✍🏻✍🏻✍🏻

*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
[1/4, 7:32 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: *🎀AKWAI BANBAM CI🎀**_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*

_*(MRS BB)*_

_*{MAGAJIYAR KAINUWA}*_


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


3/1/2020.

5&6.

Karfe hud'u nayamma za,ashiga Amma har azahar mubee ta na cikin kokonto tarasa meke Mata dad'i,
Hak'ik'a Adam yasota yanama cikin son nata ya dace tacigaba da wannan shariar,

Fitowa tayi daga d'akinta tanufi falo inda su mama suke,
Zama tayi kusa da ita tace"mama cikinku babu Mai iya bani wata shawara game da wannan sharia, kunbarni inacikin kokonto,
Shin idan akazo akagano cewar Adam bashi yayi wannan kisanba dawane ido zankallai shin zai iya cigaba da zama dani kuwa mama,
Kiyi magana nidai gaskiya nasare"

"Kikasare ubanwa,audama kina tunanin zakicigaba dazama da d'an fashi matsayin mijinki,to idanma kina wannan tunanin kiciresa,don babuke babu Adam jiranake agama wannan shariar wallahi saiya sakeki, don haka kisan dasanin dole kece zaki cigaba da kare Mahaifinki,inbacin kina sakarai taya Wanda akashe ubanki kice zakicigaba dazama dashi,to bazai yuwubah,"

Yayansu ne yashigo yace"mama kidaina tada jijiyar wuya maganar ta da Adam dama babu ita kuma dole zakicigaba da zama lowyer dady har agama wannan case d'in"

Kuka tafashe dashi tace"ni wallahi inason mijina babu Mai rabani dashi,naji xan tsayawa dady har agama shatia Amma wallahi saina koma gidan mijina"

"Zainab tace uhm yarinya kenan, Allah yasa agama lafiya basai idan zai kub'utaba"

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KOTU*

Kotun tacika mank'il don dayawan mutane sunason suji yadda wannan k'ara zata kasan ce,
Don kowa yana mamakin maizai saka siriki yakashe sirikinsa, motar y'ansanda ce tashigo dauke da Adam,
Fuskarshi tayi jawur abunka da farin mutum,daka kalleshi nan take zakasan k'yakk'yawan gaskene wuyace da wahala zata munan tashi yarame yayi duhu,

Sanye da unka haka akashiga dashi kotun saida aka kaishi inda yake tsayawa sannan akaciremai,

Iyalan Alh muhd kowa yazo harda *jannat* ba,abarota bah
Alkali yashigo duk aka Kai gaisuwa saida yazauna sannan kowa yazauna,
Yayi y'an dube dubensa da rubuce rubucensa sannan yace ina barrister Mubeenat,

"Sir am here"

"Zaku iya cigabada gabatar wa da kotu hujjojinku"

Tayi godiya takoma yadau zauna,

Barrister lawan ya mike yace"yamai sharia inason kotu tabani dama zangabatar da shaida ta akan cewar Adam bashine yai wannan kisan bah"

"Ak'ali yace kotu tabaka dama"

Yajuya yadauko wata waya k'aramace Nokia,
Tamika ma Alk'ali yace"my load kaduba kagani zakaga text message d'in da akayowa Adam damisalin k'arfe biyu nadaren ranar da aka kashe Alh Muhd"

Alk'ali yashiga dubawa yagama yaga sauran alk'alan dake k'asa, suma suka duba,

Kafin daga bisani akamikawa barrister lawan wayar,

Cikin bacin rai tamik'e tace"ya Mai sharia inason Zan gabatar da wa kotu wasu shaiduna,
Dazasu yabbatar da cewar Adam shine yayi wannan kisan,"

"Kotu tabaki dama"

Itama wayarce Amma wannan karon babbace,
Tamika tare dacewa"kaduba yamai sharia sakonnine gasunan har guda uku, sakon farko yana magana akan, cewa.

"Alh Muhd Tabbas rayuwarka ta na cikin had'ari muddin baka bani Abunda nake buk'ata daga garekaba"

Kaga kenan yamai sharia ya dad'e yana bibiyar mahaifina,
Sannan sakon nabiyu yana cewa.

"Tunda kanuna taurin Kai idan k'ak'iji bakak'i ganiba ni Adam sai nad'auki mummuman mataki akanka,"

"Anan ma yanuna k'arara cewar yana hak'e dashi ya tanadin wannan ranar tazo yakasheshi..... Hawaye suka silalo Mata,"

"Tacigaba sannan yamai sharia,sako na karshe idan kaduba yanuna zahirin cewar Wancan azzalumin shine yakashe man mahaifina,"

"Yace yashirya kwanaki kad'an yarage kwanan Sa yakare don bazai iya cigaba da bibiyarsa ba yana b'ata ma shi lokaci"

Tayi shiru ta na shashshekar kuka,

Kotun tad'auki hayaniya sosai kowa yana fad'an albarkacin bakinsa,

Adam babu abunda yake face kuka, don baitab'a tunanin cewa mubee bata k'aunarsa ba saiyau,
Ashe zata iya yimashi Sheri duk Dan biyan buk'atar ranta lallai yayarda cewar soyayyar dayake Mata batada wani Amfani,
Tabbas mubee tacucesa yanzu dawane bakin zai,I ya kallon taron mutanen nan yace baiyi bah,wama zai yarda cewar bashibane wasu hawayen suka sake silalomashi,
Yamik'a lamarinsa wajen ubangiji shine gatansa shizai shige masa gaba, idan anzalinceshi Allah yasaka Mai shashshekar kukan yake sosai,

Alk'ali ya tsawatar akai shiru yadad'e yana rubuce rubuce kafin yad'ago yace"barrister lawan koyanada A bun cewa, girgiza Kai yayi don bashida sauran wata sheda dazata fitar da Adam daga wannan kullin, shikanshi yatausaya wa Adam,
Bashida kowa shikadai yake rayuwarsa,yanzu shikenan hukuncin daurin rai darai yahau kanshi"

"Alk'ali yace Malam Adam ko kanada Ja akan wannan shaidar da matarka tabada,"

Hawaye kamar ankunna famfo haka suke kwarara daga idonsa zuciyarsa tafasa kawai take,yanzu shi mubee zatayiwa Sheri wananna wace irin mummunar ranar ce agaresa,

Bai iyayin maganaba d'aga Kai yayi yana wani irin kuka Mai tab'a zuciya"

Alk'ali yagama duk abunda zaiyi kafin yad'ago yace"Abisa shaidun damuka samu k'warara dasuka tabbatar dacewar Wanda ake tujuma ya aikata wannan laipi,
Don haka wannan kotu Mai adalci ya yiduba ga irin shaidun da suka gabata ta yankewa Wanda Ake tuhuma hukuncin d'aurin rai darai agidan kaso tare da aiki tuk'uru,
Idan masu goyon bayan mailaifi suna ganin hukuncin baimasuba daga nan zuwa farkon watan 1/1/2016. Suna iya d'aukaka k'arar zuwa kotun gaba, kotu tatashi,

*kotu* *kotu* *kotu*

*TIRKASHI,ANYA KUWA MUBEE TA KYAUTA*

*KUKASANCE DA MAMAN MUHSEEN*✍🏻✍🏻

*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*

*PLSSS COMMENT AND SHARE*✍🏻✍🏻✍🏻
[1/6, 11:43 AM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: *🎀AKWAI BANBAM CI🎀**_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*

_*(MRS BB)*_

_*{MAGAJIYAR KAINUWA}*_


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


7&8.

~bismillahir rahmanir raheem~

Kuka take natashin hankali abakin kotun bayan fitowarsu,
Ganin ankamo Adam yana cikin wani yanayi na tashin hankali za,awuce dashi gidan maza,

Dagudu ta isa wajenshi ta kamashi tarungume sosai ta na wani irin kuka natashin hankali,
Hak'ik'a jiyai wani irin sonta yazo ya mamaye ma shi zuciya,
Amman dayatuna irin k'azafin datayi ma shi Wanda yayi silar jefashi cikin wannan tashin hankalin,saiyaji soyayyar tarikid'e takoma tsantsar k'iyayya"

Wata irin hankad'ewa yayi Mata da k'arfinsa yaturata baya,
Tatafi tayi wata irin fad'uwa yanunata da yatsar Sa manuni, yace yana Mai zubar da kwalla masu zafin gaske, idonsa yayi wata irin kala,
"Natsaneki mubee, Natsaneki gabakid'aya rayuwar danayi dake inamai yin nadama, har Abadan duniya bazan tab'a yafemaki bah, kid'auka baki tab'a sanin wani Mai kalar suna Adam ba,
Zantafi gidan dakuka turani saboda rufuwar asirin uwarki, Amma kisani wallahi bazan sakeki don yanzu bah,
Kije kiyita fama da igiyar har ranar dazan koma ga Allah"

Cikin wani irin ihu da kururuwa take kuka ta na jijjiga jannat dake kusa da ita,
Nashiga uku mama kicece ni kekika sakani,
Idan baki taimakeni bah zantona asirin,
Zainab tabuge Mata baki har yayi jini.....
Y'ansanda suka turashi cikin motar sukatai dashi.

Kuka take sosai zagikam tashasi wajen mama,
"Cewa take don ubanki cikin taron mutane zaki fallasani, saboda ba kisan ciwon kanki ba kinzab'i namiji akan iyayenki,to sai inga ta inda zaku iya kasancewa don ubanki,
Kuma da karfin bala,i saiya sakeki don bazan had'a zuria da d'anfashi da makamiba,"

Yayansu sama,Ila shiya ciccib'eta yasaka ta mota sukabar wajen,
Yan jarida kuwa sukasamu rahoto don dama k'iris sukejira,

Jannat tunda take bata tab'ajin tausayin Adam bah irin yau,
Hakika akwai abunda yafaru kuma inhar ni lawyer ce Mai zaman kanta nayiwa Kai na alkawarin ganin Adam yakub'uta daga wannan zalincin da akaimashi wannan yanuna bashine yayi bah, d'oramai akai.

Tunda suka koma gida mubee bata da aiki sai kuka,
Bata da magana sai ta Adam,
Sabbatu kuwa idan tafara sai mama ta Mata shegen duka sannan takeyin shiru,
Don sakin layi take sosai ta na fad'ar magan ganun da sukayi cikin sirri da mamai,

Cikin kwana biyu idan kaga Adam saikayi mashi kuka saboda halin dayake ciki,
Wahala akebashi iyawuya yayi wata irin rama da baki,
Baya cin Abinci saboda yanzu bayada wani burin dayawuce mutuwa,

Yau jabeer yazo wajensa yakuma roki Wanda yakawoshi arzikin yabasu isashen lokaci don magana ce zasuyi Mai yawa,
Yak'iya harsaida jabeer yabashi kudi sannan yabasu awa d'aya da rabi,

Hawaye suka ringa zubowa jabeer ganin abokinsa kuma gudan jininsa cikin wannan halin,
Baisan sadda yafashe da kukaba don yarasa ma ta ina zaifara,
Kukan dayake shiyasa Adam d'inma yinnashi,

Daker suka lallashi juna Sukai shiru,
Jabeer yanisa sannan yace"Adam babu isashen lokaci don haka dole zamuyi komi kan lokaci,don kaga kwanaki k'adan yarage lokacin da akabamu yawuce"

"Sannan inason matai maki akallah insamu lawyer maizaman kanshi, Wanda yasan aikinsa dole zamu d'aukaka karar zuwa kotun daga ke sai Allah ya isa,
Watau kotun abuja"

Share hawayensa yayi yace"jaber dazakaji tatawa kakyale ni kawai na idasa rayuwata anan, banajin zamu kuma yin nasara saboda makiya bazasu kyalemu bah"

"Aa indai ina numfashi da lafiya ta Adam bazan iyabarinka cikin wannan yanayin bah"

Donhaka zanje nasamu lawyer babba zamu tattauna konawa yakeso zanbashi indai zai tsaya mana, don haka dole idan nazo dashi kafayyace komai, babu batun b'oyo don muna son mutseratar da rauwarka"

"Yarausayar dakai yace to jabeer nabaka wuk'a da nama,kayi duk yanda kaga yadace banda Abunyi"

"Shikenan zantai yanzu bazan koma hotel bah har sai nasamu ganawa da lowyer,idan mun had'u zuwa gobe zanzo dashi"

"Nagode jabeer na go........."

"Haba mana Adam babu godiya tsakanin mu duk abunda zanmaka zanyishine bisa don yazama dole na don haka kabar godeman Addua zakayita yi Allah yabamu Sa,a"

Sunyi bankwana kamar karsu rabu, Amma haka yatafi yana Mai tausayawa Adam halin dayake ciki, rayuwa ta na juyawa dashi wani iri.

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

"Mubee ina wayarki don Allah"

Wani banzan kallo tayi Mata tace"ubanme zakiyi da wayata kuma"

"Ke karki zagan daga tambaya, bafa ni nakar zoman bah idan dakin bi shawara ta aida duk haka bata faruba,ni babu Abunda zance face Allah yak'ara"

Cikin jin haushi da bak'inciki kalaman ta,
"Tace don kutumar uwarki nikike Allah yak'ara lallai nayarda ke mak'iyya tace,
To Dan uwarki duk bak'in cikinki da Mijina yafi k'arfinki"

Dariya tayi tace"oho dai abanza tunda agaban dubun mutane yace baya sonki,takwashe da dariya"

Azafafe tataso zata kamata da kokowa taja baya"karki fara don ni bazan k'ara had'a jiki dakeba Karna gogi mugun hali"

Haka sukaita hayaniya har mama ta shigo tace"to sababbu ubanme yafaru kuma"

Fashewa tayi dakukan munfurci tace"mama wani jannat takecewa bak'in halin dana gado wajenki yasaka najefa mijina cikin wani hali, daga natanka tarufeni danduka"

Ai mama najin haka tayi kan jannat zata hau kila kamar Allah ya aikota,
Amma ina jannat tace wallahi bazan zauna kuyita dukana kamar jakar kuba,
Taruga tafita daga d'akin tashige nata ta kulle"

Mama sai masifa take"aidama zaman Alh kike ko to yamutu don haka wallahi kizo kikoma can ruga inda akecin tuwan dawa miyar kuka,"

Dariya jannat keyi ita d'aya tace oho dai Amman nagama zama kumaidani jakka wallahi,

Wayar tace tayi k'ara takwanta agadonta sannan tajawota,
Tadauka tare dayin sallama,
"Rankiyadade Aiki yataso na gaggawa don yanzu haka ga wani bawan Allah nan yana son ganinki,don wata sharia ce Mai rikita Kai ce tagagareshi kuma anbasu lokaci don d'aukaka k'ara"

Ajiyar zuciya tai tace"wayeshi"

"Sunan sa jabeer....."
"Nagane shi kabashi no. D'ina yakirani muyi magana"

"To rankiyadade"

Taka she wayar tace"cikin sauki dama no. D'in ka nakeson na d'auka cikin wayar waccen sakarar."

Babu jimawa yakirata,
"Bayan sungaisa take cewa malam jabeer yakuma akaji da wannan Abu"

"Yace to angode Allah Amman jannat babu wata damuwa kuwa, naga yan gidanku sune masu wannan sharia"

"Manta dasu ni nayi niyyar taimakon Abokinka bakuma don halin Saba, badan komiba saidan bazan iya jure ganin irin wannan zalincin bah,
Don haka babu Wanda ya isa yadakatar dani kaje afitar da jaridar d'aukaka k'ara
Sannan kashirya kaje kotun don anso takardar sammaci kakawo masu nan gidan,

Kafi nan dole muna buk'atar hujjoji masu kyau,
Muhad'u dakai da yamma bayan sallar la asar,
wajen magama resturence"

"Shikenan jannat nagode sai mun had'un"

Sukai sallama taka she wayar.

*TO FAH YAKUKE GANIN WANNAN SHARIAR*

KUCIGABA DA KASANCEWA DANI,
MAMAN MUHSEEN✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE PLSS*
[1/8, 6:04 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: 🎀🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBAN CI*
🎀🎀🎀🎀*_DAGA ALK'ALAMIN_*
👇🏻


*_AISHA ABUBAKAR_*
*_{MRS BB}_*

*_MAGAJIYAR KAINUWA_**بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.~

9&10.

bawata kwalliya tayi bah hasali ma jannat kwalliya bata dameta bah,
Zata dai saka powder da kwalli sai man baki, ko janbaki bata sakawa balle wata pull make up,

Doguwar rigace tasaka tayi rollyn da babban gyale daya rufe Mata kirji,don Masha Allah tanada albarkatun su.

Jikkarta tad'auka tafito don wayarta da komai naciki,
Afalo tagamu dasu suduka banda mubee,
Don tunda akagama shariar bata yawan zaman falo,

"Gidan ubanwa zakije ehy"

"Mama aikin gaggawa yataso man bazan jimaba zandawo"

"Kima kwana can don ubanki, ni
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment