Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBEYou Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namuAlura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOCMasu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our servicesNote that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame usNote that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download itNote that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTThis Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

CUTA TA DAU CUTA
.
DANDANO
.
Nazir Adam Salih (Nas)
.
Ka manta. Tace.
Ba nan bane hanyar, dogon saurayin ya juyo ahankali ya dubi fuskarta sannan yace.
Ai na sani. sannu ahankali sai taga kamannin fuskarsa sun fara jirkicewa tamkar yadda ruwa ke jirkita yayinda ka watsa masa garin zabibi aciki.
.
Nace da kai ba nan bace hanyar! Ta sake cewa dashi wannan karon a firgce tana dubansa. Ga mamakinta saitaga ya rike sitiyarin motar da hannu daya. Dayan hannun kuma wukace zungureriya tana kyalli. wayyo!!! Budurwar ta kwalla ihu saurayin ya sake dubanta cikin murmushi yace. Kada ki damu
KASHE KI ZANYI AHANKALI CIKIN TAUSAYI BATAREDA KIN SHA WUYA BA.
.
Nazir Adam Salih (Nas)
.
CUTA TA DAU CUTA-01
.
(m) Nazir Adam Salih.
.
(c) Yarima Gangariya
.
LITATTAFAN NAZIR ADAM SALIH.
* Kibiyar Ajali
* Meyafi Kudi
* Ta Leko Ta Koma
* Birnin Sarauniya
* Naira Da Kwabo
* Aci Bulus
* Aljani Ya Taka Wuta
* Damisar Takarda
* Bindigar Kwali
* Wa Na Kama?
* Kai Da Jini
* Kudi Da Maciji
* Iska Mai Kada Ruwa
* Cuta Ta Dau Cuta
.
GAISUWA GA..
Kabuga Readers Association
Ibrahim A. Sadeeq
Sani Datti
Bashir Ibrahim
Isyaku M. Sadi
Mamunu Gambo
Usman A. Mudallah
Nazeer Sadeeq
Hajeeya M. Saifullah
Anas Umar
Sunusi Ya Sayyadi
Magaji (Taliban Naira)
Auwal Zakariyya
Sani Inusa Abubakar
Salisu Yahaya.
.
CUTA TA DAU CUTA
Copyright (c) Nazir Adam Salih 2001
Hakkin Mallaka (h) Nazir Adam Salih 2002
.
TARIHIN DABI'INSA.
Anfara Bugashi A Jet Age.
.
Gargadi Ba'a yarda wani ko wata kungiya ba tayi amfani da kowane irin sashe na wannan littafi ta hanyar wasan kwaikwayo ko kuma wani abu daban saida izinin marubutan.
.
ADIRESHI.
Abubakar Sadiq Islamiyya
P.O BOX 4792 Dakata Kano State.
.
TSARA RUBUTU.
Umar Mohd. (Monnetor) Sauna
Standard Vision Nigeria Ltd. (Computer)
.
CUTA TA DAU CUTA
Nazir Adam Salih (Nas)
.
NAS 2002
.
YAN DABARU.....
Adaren wata zazzafar lahadi ne cikin watan maris na shekarar miladiyya wata mashaya dake dab da bakin wani kogi ta dinke dankam da yan birni sunata bushasharsu da sharholiya kai kace bazasu mutu ba KWATSAM Sai Akaji Wata Mata Ta Kwalla Ihu.
.
(Yarima Gangariya)
Ku Biyo NiCUTA TA DAU CUTA-02

(m) Nazir Adam Salih

(c) Yarima Gangariya (Jikan Sidi)

Kwarsam sai akaji wata mata ta kwalla ihu.
Nan da nan sai kusan mutanen dake gurin suka juya zuwa ga kallon matar cikin mamaki. Domin matar a zaune take ita da saurayinta na bariki hakanan kuma ba'a cikin layin yan rawa take ba ballantana ace wani ne ya taka mata kafa take kwakwazo.
Ah! Cikina matar tace cikin karaji hannayenta rike da cikinta ba'a dade ba kuma saita fara sheka amann giyar data sha har iya wuya.
Hahaha! Wani saurayi can cikin yan rawa ya kece da dariya sannan yace.
Aikin banza malam wallahi wajennan yafara baci da ajawuna dubi dan Allah wani tsamin gaye yadda ya kawo mana wata ajawuwar bebi tasha giya sai bata wa mutane guri takeyi da amai to da ubanwa yace tasha bayan tasan bazata iya rike wuta ba.
Tuni sauran mutanen dake mashayar sun maida hankalinsu ga sharholiyarsu hakanan yan tsirarrun dake daf da teburin da matar take duk sun matsa nesa da ita don gudun kada ta bata musu gogaggun kayan cinyewarsu da aman giya.
Saurayin dake tare da matar ya mike tsaye cikin takaici kwalbar giya ahannunsa yana duban matar dake kwance tana murkususu da kururwa.
Daga can kuryar mashayar inda anan kofar shiga da'irar sharholiyar take wani dankareren mutum mai kirar yan dambe ya nufo inda saurayin da matar mai murkususu suke yana wasa da kwanjinsa ta cikin matsatsttsiyar suwaitar dake jikin nasa baka akirjinta an rubuta da manyan haruffa TWO IN ONE.
Meke faruwa ne buros? Katon mai kirar yan dambe ya tambaya yana duban saurayin cikin zargi.
Wannan jemagiyar ce kawai malam tasan bazata iya dauka ba tasha giya tai mata yawa. Ni na ma rasa yadda zanyi da ita katon ya sake duban saurayin cikin damuwa yafara shawarar yayi musu korar rashin arziki shida yarinyar tasa. To amma sa'ar daya tuna da cewa saurayin fa lokaci lokaci yakan dan yi masa abin alheri saiyaga bai dace ba ya dauki wannan matakin dan haka sai yace.
Kaga fa bama son wani abu da zai korar mana kwartamomi domin zuwa da irin matan nan na iya korar mana mutane dubi fa yadda ta bata mana guri da amai yanzu in banda Allah yasa ma duk kuwa kowa a buge yake da tuni duk sun fice daga mashayar. Gaskiya yakamata kasan da irin matan da kake taku.
Wallahi nima tsautsayi ne kuma gani nayi Bebi din akwai (Face) shine ta dau hankalina saurayin yace yana dan murmushi amma har yanzu dai kana ganinsa kasan ransa a bace yake meyiwuwa kuma ga dukkan alamuba abinda yarinyar tayi masa bane kawai ke damunsa akwai wani abu.
Bakomai bari in kirawo yara su fice ma da ita. A ina ka daukota? Katon ya tambayeshi saurayin ya saki wani tattausan fito gamida shafar kyakkyawar fuskarsa da hannayensa yace.
Anan bakin city hotel na daukota.
Kana nufin kace anan dakinta yake? Katon yasake tambaya.
Nima abinda nake tambayar kaina kenan kaga ni dai kawai dan Allah taimaka kasa su mayar da ita can kawai su jefar da ita shikenan mun rabu. Kafin nan da asuba dai ta farfado. Jin haka daga bakin saurayin shiyasa katon dariya sannan sai yayi fito sau uku fit fit fit. Wasu manya manya guda biyu duk masu kirar yan bori suka fito daga wani dan lungu dukkansu masu gadi amashayar ne hakanan kuma sukan tausasa duk mashayin daya so yin haukar rainin hankali agurin.
Ku dauki wannan shirmen ku jefar da ita a city hotel.
Katon yace da kartin biyu lokaci guda kuma ya nuna matar da haryanzu ke kwance tana ta keta amai. Kartin basuyi wata wata ba sai suka dauketa sakayau kai kace gadon kara suka dauka sukayi waje da ita.
Nagode fa saidai kuma ina ganin sai gobe idan nazo ma hadu saurayin yace yana shafar aljihun doguwar rigarsa.
Ah! Ba komai ai muna tare katon yace sannan da murmushi gamida sarawa saurayin saiya juya ya nufi kofar mashayar inda yake zaman tsaro kwanjinsa na barazanar fesa rigar dake jikinsa.
Har katon yabar gurin saurayin na nan tsaye hannunsa cikin aljihiun doguwar tazarcensa yanata wasi wazin zuciya domin daganan baisan inda zashi ba dan aljihunsa a bushe yake karaf babu ko karfuna aciki.

Wannan saurayi dake tsaye shi da kudi manyan abokan gaba ne domin ko shi kansa kudi yasan yana tsoronsa bawai baya samun kudi bane a'a yana samu to saidai kuma bariki bata barin kudin su taru hakanan kuma bashida aikin fari balle na baki to amma duk da haka mafi yawan lotuka yana cikin kudi wanda hakan shi ya gagari tunanin jama'a da dama da suka san saurayin
mafi yawa daga cikin kudaden da saurayin kan samu yakan neme su ne ta hanyar yan dabaru alal misali in har yaso yana iya tashin mota kota uban wacece ya tukata kuma koda babu dan makulli hakanan kuma acan cikin kasuwar tsaye tabayan gida akwai dilallan dare mabukata wanda zasu bashi rabin kudinta na asali atake agurin batareda kuma sun tambayi inda ya samota ba. Yayi nasa guri batareda tada jijiyar wuya ba. Har ila yau saurayin kan iya bin duk wanda ke dauke da jaka ta kudi abaya abaya zuwa gida atake agurin zai kirkiri yan dabarun da zai raba mutumin da kudinsa batareda shan wuya ba. Idan kuma duk wannan bata samu ba to awasu lokutan yakan shiga gungun yan fashiCUTA TA DAU CUTA-03

Awasu lokutan yakan shiga gungun yan fashi masu bukatar kudin gaggawa shima ayi dashi to amma har zuwa yanzu sau uku kawai aka taba kai hari dashi suma din saida manyan mafasan sukayi masa alkawarin baza'a kashe ko mutum daya ba domin duk rashin imaninsa shi bai yarda da yayi kisan kai ba bakuma wai dan tausayi ko imani ko kuma wai dan bazai iya bane a'a saidan cewarsa hanyace mai hadari domin da zarar an kamaka to kai ta kare maka kenan to wannan ita tasa saurayin ya ware kansa gefe guda yake ci da yan dabaru wasu lokutan har yakan hada da damfara domin idan ka dubi kyakkyawar fuskarsa ma'abociyar murmushi kowane lokaci saiya yaudareka ka dauke shi amatsayin wani babban lauya kokuma ma'aikacin gwamnati.
Dan haka koda ya zura hannunsa ayanzu cikin aljihunsa yaji babu ko kwabo sai zuciyar ta hasko masa hoton bayan wata mota kirar honda daya hango sa'ar da suke shigowa mashayar shida yarinyar ko shakka bayayi akwati ce yagani baka kuma yasan zaiyi wuya in har ba kudine aciki ba domin shi kansa yasha zuwa bariki da tulin kudi cikin jaka domin kawai ya burge mata.
Acan gefe guda samari da karuwan gidan dana daji sai chashewa suke abinsu sunyi layi sahu sahu anata dansewa wasu ko sai kora ruwan bagaja suke abinsu.
Saurayin yayi ajiyar zuciya sa'ar daya kawo karshen wasiwasin dayake sannan saiya nufi kofar fita daga mashayar koda yakai kofar sai katon nan mai tsaron kofar ya washe baki cikin murmushi yace.
Ya akayi ne Buros tafiya haka zakayi yau da wurwuri. Saurayin yayi dariya sannan yace.
Ai yau banji dadin zuwa ba gara na ware sai gobe kuma. Ina fatan bazaku dawo tare ba. Katon yace cikin dariya.
Kai Allah ya tsari gatari da saren shuka. Saurayin yace lokaci guda kuma ya nufi filin da aka tanada akofar mashayar domin fakin da motoci.
Filin fakin din cike yake dankam da motocin yan birni wanda kusan kashi saba'in daga cikin dari na motocin dake gurin duk honda ne da toyota saurayin ya nufi filin fakin din kai tsaye babu alamar tsoro ko fargaba idan ka ganshi saika rantse da Allah shima motarsa ya ajiye agurin zai dauka akayi kuma babbar sa'a gurin fakin din cikin duhu yake domin katuwar baranda ce ta kwano wacce ke dauke da kan lantarki kwaya daya jal kamar rai kuma shima jan kwai ne bamai haske ba. Meyiwuwa hakan nada nasaba ne da irin yadda manyan mutane kan ziyarci mashayar wanda kuma basa bukatar kowa yasan da zuwansu domin ganinsu agurin na iya sawa suyi girman Kwabo.
Koda saurayin ya isa tsakiyar jerin motocin saiya fara waige waige amma batareda ya tsaya guri guda ba domin yasan yin hakan na iya janyo masa zargi ga duk wanda yazo wucewa tunda dai ansan in har ba motarka ka ajje agurin ba baka bukatar waige waige kana zuwa kasan inda ka ajiyeta.
Adaidai lokacin da saurayin yafara fargabar ko mai motar ya dauke abarsa sai ya hangota acan kusan karshen filin fakin din tsakanin wasu motoci guda biyu kirar Nisan da Lancer.
Zuciyarsa na harbawa tsakanin hakarkarinsa amma jikinsa baya rawa saurayin ya nufi inda motar take kai tsaye kai kace tasace yana zuwa saiya durkusa ajikin motar ya boye kansa gaba daya wanda koda tsautsayi zai jefo da wani ma bazai taba iya hango shi ba kuma ga duhu ma.
Saurayin ya lalubi aljihunsa ya dauko wani dan karamin karfe mai siffar abin sakatar hakori sannan cikin sauri saiya zura shi cikin yar kafar dake jikin kofar motar yafara jujjuyawa cikin gwaninta da sabo na yau da kullum ba'a fi mintuna biyu ba sai kofar motar ta bude wadda zuwansa gurin duk a rufe suke.
Saurayin yayi ajiyar zuciya gamida share gumi dake wanke masa fuska sannan a durkushen batareda ya mike tsaye ba saiya bude kofar ahankali ya leka bayan motar zuciyarsa ta harba das das har sau wasu adadi sa'ar daya hangi duhu duhun jakar wacce haryanzu ke ajiye abayan motar. Nan da nan ya mika hannu ya janyota abinsa sannan cikin sauri ya maida kofar ahankali ya rufe. Saurayin ya jingina jakar ahannunsa tabbas kudine aciki domin shi da kudi alkawari ne indai suna guri to dafawa kawai zaiyi yagane sune.
Yayi murmushin samun nasara sannan saiya mike tsaye zai tafi.

Dauki kudin ka ajiye min jakar domin nafi kaunarta da kudin.
Wata busasshiyar shakakkiyar murya tace dashi daga can baya. Sannan sai yaji wani siririn hannu tattaura ya dafa kafadarsa kamar rodi.
Zazzage kudin cikin aljihunsa ka barmin jakata nace ko bakajin hausa ne? Aka sake maimaitawa.

**** ***** **** **** **** ********* **************

Tun da saurayin yake ba'a taba kamashi dumu dumu cikin sata ba haka nan kuma tun da yake bai taba girgiza irin wannan ba. Tun kafin ya juyo yaga mai maganar gumi ya fara wanke masa fuska dakyar yake numfashi. Ahankali jikinsa na rawa saiya juyo sukayi ido hudu da mutumin adaidai lokacin da jakar ta subuce daga hannunsa.
Dan me zaka jefar min da jaka?
Nace dakai ka debe kudin kabani jakata ko to ko so kake ka batamin rai nayi ma ihun BARAWO?
Mutumin ya sake cewa saurayin ya dubi mutumin saiyaga kamar ya balle saboda siranta dogo ne sosai kamar ya karye saboda tsayi hakanan kansa kankani ne wanda ya dace da uban jikin...CUTA TA DAU CUTA-04

Dogo ne sosai kamar ya karye saboda tsayi hakanan kansa kankani ne wanda ya dace da uban jikin.

Idanunsa kanana kamar na kumurci bakinsa tsukakke hancin kuwa kamar na aku kuturu sannan kuma siririn mutumin sanye yake da kwat da wando farare kafarsa cikin bakin takalmi hakan kuma dogayen hannayensa sanye suke cikin aljihun kwat dinsa duk wannan saurayin ya kula dasu ne lokaci guda sa'ar daya juyo.
Ka.... Rufamin asiri dan Allah saurayin yace muryarsa na rawa.
Kada ka bada ni mana DA'U FATAKEN dare kaida tuni ma har kafara burgeni amma kuma kake kokarin ragemin karfin gwiwa nifa banason matsoraci saurayin ya dubeshi baki bude kuma a rude cikin rashin fahimtar inda dogon mutumin mai kirar langa langa yasa gaba.
Ban fahimceka ba saurayin yace ga mamakinsa saiyaga dogon mutumin yayi murmushi
kada kaji tsoro ko fargaba da'u fataken dare na dade ina neman kwararre kamarka bansamu ba sai yau gashi abanza na tsinci dami akala. Dogon mutumin yace gamida sake murmushi sannan saiya dada da cewa.
Dauki jakar kazo mu kebance ina ganin nan ba gurin da zamu tattauna cikin dadi rai bane. Ya sunkuya ahankali tun kafin saurayin ma yasami damar sake magana ya dauki jakar kudin ya mika masa.
Dubu ashirin da biyu ne kawai kafara tabawa Allah yasa rabon kane.
Biyoni mu tafi. Mutumin ya juya abinsa ya nufi can wani bangare daban daga arewacin mashayar. Saurayin yayi kerere cikin rudani dauke da jakar ahannunsa sannan da yaga mutumin yaci gaba da tafiya sai wata zuciyar tace dashi kai dan samari tsoron me kakejine? Bishi mana kaji abinda zai fada maka ai mai rabon gani badi ko ana ruwan kibiya saiya gani waya sani ma ko kaci bulu. Tunanin hakan keda wuya sai saurayin yabi dogon mutumin abaya cikin sauri har ya cimmasa adaidai lokacin daya karasa ga wasu shuke shuke dake bayan mashayar mutumin yayi murmushi sa'ar dayaji saurayin na biye dashi.
Ko kaifa dan samari amma da ina yabonka sallah zaka kasa alwala.

Dogon mutumin na gaba saurayin na binsa abaya lokaci guda kuma zuciyarsa nata kai kawo da dimbin wasi wasin dan siririn mutumin domin akwai wani abu a tattare dashi da saurayin baya so. Hakanan kuma zuciyarsa sam sam bata amince dashi ba domin haryanzu kallon mahaukaci yakeyi masa saurayin ya sake duban rekeken wuyan mutumin saiyaji kamar ya fashe da dariya domin yasan koda wani sharrin yake shirin kullawa to babu yadda zaiyi dashi.
Ina ganin nan ya ishemu mu tattauna abinmu cikin sirri batareda wani ya saurari jawabina ba. Mutumin yace sa'ar da suka kawo gindin wata katuwar bishiyar dorawar turawa.
Dogon mutumin ya zauna akan wani dan benci wanda daman kamar su yake jira hakanan shima saurayin ya zauna daga inda suke zaune suna iya jiyo hayaniyar mashayar sunata hargowa da ife ife cikin nishadi ga sautin gangar nasara sai tashi yake cikin daren.
Koda saurayin ya zauna sai dogon mutumin ya dubeshi yace.
Nawa zan cika maka akan adadin dana baka yanzu idan ina son ka
KASHE MIN WATA KYAKKYAWAR BUDURWA WACCE DALIBA CE AWATA MAKARANTAR KWANA.....?

CINIKIN RAI...
Saurayin yaji kamar katanga guda ta fado masa atsakiyar baya sa'ar da amsa kuwwar kalaman dogon mutumin ta doki dodon kunnensa.
Ayanzu kam ya tabbata zaton da yakeyiwa mutumin yazama gaskiya ko shakka bayayi yasan MAHAUKACI ne dan haka abinda yafi kawai shine yayi kokarin su rabu lafiya yace da kansa.
Ina ganin da zaka rike jakar kudin ka banni nayi tafiyata nida yafi min duk wata kyauta da zakayi min
saurayin yace lokaci guda kuma ya mikawa mutumin jakarsa yana kokarin mikewa tsaye.
Kada ka gudu dan saurayi nasan abinda nake tunani ka dauka ni mahaukaci ne ko? To bari kayi yau lahadi sha biyar ga watan maris hijira alif dari tara da casa'in da uku
ina fatan yanzu ka gamsu ina da hankalina ko? Mutumin yace gamida sakin wani shekrarren murmushi wanda da gani ba kasafai ya cikayinsa ba sai airin wannan ranar saurayin ya kura masa ido yana kokarin karantarsa daga karshe dai ya yankewa zuciyarsa cewa lallai kam kamar kuma mutumin na da hankali.
To in kuwa da hankalinka dan me zakace na kashe maka mutum? bayan kuma ko ganina baka tabayi ba? saurayin ya tambaya.
Inada hujjar duk wani abu dakaji na fada. Dan siririn mutumin mai kamar langa langa yace sannan saiya lalubi aljihunsa ya fiddo da kwalin sigari (Rothman) Ya mikawa saurayin sannan suka cinna wuta.
Nayi matukar mamakin abinda yasa kyakkyawan saurayi kamarka kuma kakkarfa ga kuruciya amma ka tsaya kake bata lokacinka akan yan kananan sace sace.
Yace yana duban saurayin ganin baice komai ba saiyaci gaba.
Yau kusan kwana ashirin da biyu kenan ina neman mutumin da zai iya kashe min wata yar budurwa amma na rasa domin duk wanda na kalla sai inga baiyi daidai da irin zaman duniyata ba sai yanzu ka fado kan hanyata abanza. Kowa ya dubeka zaisan kyawunka da karfinka da kwarjininka na iya kai mutum ga miliyoyin masu gidan rana. Amma abin mamaki saigashi kana ta bata lokacinka agurin dauke dauken yan kudin da ko kyautar gwamnati ma basu kai ba. Mutumin yayi shiru sa'ar da saurayin ya muskuta yana shirin.CUTA TA DAU CUTA-05

Saurayin ya muskuta yana shirin fadin wani abu.
Nakasa fahimtar inda maganganunka suka sa gaba da zaka fadi abinda kake sonyi bayani akai tsaye dayafi. Amma ka tsaya sai maradona kakeyi da tunanina. Dogon mutumin yayi dariya sannan yace.
Kafin nabaka labarin inason naji daga bakinka shin idan na bar maka kudi na dake gurinka ayanzu nakuma kara maka naira Miliyan guda zaka iya kashe min ita?
Wai wacece ne nifa bangane ba. Saurayin yace kirjinsa na dakan uku uku saboda zancen miliyan daya dayaji.
Don haka ai nake son ka saurara da kyau na fahimtar dakai domin tun sa'ar dana ga ka bude motata cikin yan mintuna batareda dan makulli ba na tabbata kaine irin mutumin danake nema to amma haryanzu inason kayi min alkawarin shin zaka iya kashemin ita din? Saurayin yayi shiru yana wasi wasi tuni har gumi yafara wanke masa fuska. Hakika kam mutumin yafadi gaskiya lallai kam ya dade yana aikin banza amma haryanzu bai tsallake daga ajin dayake ciki ba to amma yasan da naira miliyan guda komai na iya faruwa.
Bawai miliyan guda din kawai zai barka da ita ba in dai har ka amince abin ya cimma nasara to ina tabbatar maka da cewa nidakai mun riga mun huta hutu mara iyaka to amma kafin nabaka yadda abinda me kake gani?
Saurayin yayi shiru yana duban samaniyar ma'abociyar taurari ko ina burjik kamar fararen furanni cikin korayan ganyayyaki hakanan kuma yana sauraron hayaniyar dake fitowa daga mashayar tana ratsa shirun dake zazzafen daren lahadin.
In kuma kana ganin bazaka iya ba to ajiyemin jakar kudina daka sata kayi tafiyarka saika manta da duk wani abu danace maka haka nan nima zan manta da satar dakai min. Saurayin ya dubi kereren mutumin sannan sao yayi murmushi yace.
Ba sai kayi barazana ba kaidai fadi jawabinka nidai ban taba kashe koda akuya ba to amma.... In dai... Da gaske kake zaka bani miliyan daya... Ina ganin ka iya yin jawabinka tunda dai nasan jinsa bazai kasheni ba.

**** **** **** *** **** ********** ******** *******

Sunana SHARORO dan farin mutumin yace.
Me yiwuwa kaji sunan banbarakwai kamar sunan wani aljani ko amma akalla dai haka na tashi naji mutane suna kirana domin ahannun wani mai unguwa na girma dan ance wai ba'a san ubana ba kuma uwata ce ta jefar dani ta gudu.
Amma kafin ta jefar dani din an tabbatar da cewa da sharoro take kirana. Ya busa hayaki sama sannan yabishi da kallo lokaci guda kuma yaci gaba da cewa
Ayanzu haka ina da mace daya da Da daya hakanan kua inada hali daya halin kuwa shine tunda allah ya halicceni bana son wahala ina kuma da makwabci wanda kuma aminin mahaifiyata ne to amma bana kaunarsa daidai da kwayar zarra duk dayake dai azahiri bantaba nuna masa hakan ba kasan abinda yasa? Saurayin ya girgiza kai yana duban mutumin cikin mamaki da kaduwar jin kalaman dake fita daga bakinsa
nataba shiga cikin wani irin matsanancin hali babu magiyar da fadancin da banyi masa ba amma yaki agaza min saida ya zamana da kyar nake samu naci abinci sau daya arana kayana duk suka lalace saida tsummokara nake yawo acikin gari kamar mahaukaci nayi iya kokarina akan nasamu aiki koda naci da karfi ne to amma abin yaci tura domin idan ka dubeni dakyau zaka amince da hakan dan babu alamar karfi ajikina ka ganni tunda uwata ta haifeni ahaka nake kamar langa langa haka nayita wahala alokacin kuma fa danake baka wannan labarin ina matashi ne kamar kai.
To saidai ni ban sami damar yin karatu ba domin kamar yadda nafada maka abaya mahaifiyata kawai aka sani ba'a san ubana ba hakan shiya dada taimakwa jen rasa aikina domin duk mutanen unguwar sun tsane ni wai ni shege ne banida uba dan haka duk wanda na rabi gurinsa awancan lokacin domin ya taimakamin saikaga yayi min kora da hali suna cewa wai waye taimaki dan shege wanda uwarsa ta kasance karuwa.
Mutumin yayi shiru lokaci guda kuma sa'ar da wata mota ta fitop da gudu daga filin fakin din kofar mashayar kamar an harbota. Haskane

Please Login or Register in order to submit comment